Wasu alkaluma da aka fitar a Juma’ar nan sun nuna yadda jimillar hajojin da masana’antun kasar Sin ke samarwa ya karu sama da hasashen da aka yi na kaso 5.7 bisa dari a shekarar nan ta 2024.
Alkaluman da aka gabatar yayin taron kasa na tattauna ayyukan da suka shafi masana’antu da fasahar sadarwa na 2024, sun nuna yadda tattalin arzikin masana’antun kasar Sin ya ci gaba da bunkasa bisa daidaito, duk da tarin kalubale da ake fuskanta, yayin da a shekarar ta bana gudunmawar sashen jimillar hajojin da masana’antun kasar Sin din ya samar ga GDPn kasar ya ci gaba da bunkasa bisa daidaito. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)