A lokacin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, kasuwar kayayyakin masarufi ta kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa ta biyu mafi girma a duniya. A bana, ana sa ran yawan sayar da kayayyakin masarufi a cikin al’umma zai haura kudin Sin yuan tiriliyan 50.
Matsakaiciyar gudummawar da yin sayayya za ta bayar ga habaka tattalin arzikin kasar a mizanin shekara ta kusa kai kaso 60%. Kana, kasuwar kayayyakin masarufi mai girman gaske da matukar inganci tana ba da goyon baya mai karfi ga ingantaccen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
Tun daga farkon shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, kasuwar kayayyakin masarufi ta kasar Sin na ci gaba da habaka. Jimillar sayayyar kayayyakin masarufi ta karu daga yuan tiriliyan 39.1 a shekarar 2020 zuwa yuan tiriliyan 48.3 a shekarar 2024, tare da samun matsakaicin ci gaba da kaso 5.5% a mizanin shekara.
A bangaren kimanta cikakkiyar darajar da aka samu kuwa, jimillar sayayyar kayan masarufi a kasar Sin ta yi daidai da kusan kashi 80% na wadda ke kasar Amurka.
Sai dai kuma, ta fuskar karfin sayen kayayyaki na hakika, bisa kididdigar bayanai da lissafin da Bankin Duniya ya bayar, girman kasuwar kasar Sin a bara ya ninka na Amurka sau 1.6.
Ba wannan kadai ba, hatta ita ma kasuwar sayar da kayayyaki ta shafin intanet ta kasar Sin ta kasance mafi girma a duniya tsawon shekaru 12 a jere, kuma adadin cinikin motocinta ya zama na farko a duniya tsawon shekaru 16 a jere. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp