Dakarun rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) da ke aiki a yankin Neja-delta (ODF) sun samu nasarar ganowa tare da tarwatsa haramtattun Matatar Man fetur guda Bakwai a jihar Ribas.
A wata sanarwar manema labarai da daraktan yada labarai na sojin saman Nijeriya (NAF), Air Cdre Edward Gabkwet, ya fitar, ya ce, Jiragen yakin sun kaddamar da hare-haren ne a Cawthorne Channel da Bille da ke karamar hukumar Degema a jihar Ribas.
Ya kara da cewa, Jiragen a ranar 15 ga watan Satumba sun tarwatsa haramtattun wuraren tace mai guda hudu a Cawthorne Channel tare da bukkoki na kwana hade da rumbunan ajiye haramtattun kayan da suka tace.
Kakakin na NAF ya kara da cewa, jiragen sun kuma yi lugudun wuta a Bille a ranar 16 ga watan Satumba har zuwa safiyar ranar 17 ga watan Satumba biyo bayan gano wuraren da ake tace mai ta barauniyar hanya.
Ya kara da cewa a daya daga cikin wuraren, an samu wani karamin Jirgin ruwa da ake zargin da shi ake safarar Danyen man inda shi ma nan take aka tarwatsa shi.