Wani jirgin sama mai zaman kansa a daren ranar Juma’a ya yi hatsari a filin jirgin saman Samuel Ladoke Akintola da ke Ibadan, jihar Oyo, kamar yadda LEADERSHIP ta samu rahoton faruwar lamarin.
Jirgin mai lamba HS25 yana dauke da ministan wutar lantarki na Nijeriya, Adebayo Adelabu, da wasu mataimakansa.
- Ku Yi Aiki Tukuru Ko Na Kore Ku, Tinubu Ga Ministoci
- Sharhi: Lokaci Ya Yi Da Tinubu Zai Fuskanci Matsalolin Nijeriya
An rawaito cewa jirgin ya baro filin jirgin saman Abuja zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo da misalin karfe 6:41 na yamma, inda jiragin ya kwace ya fada cikin wani daji kusa da filin jiragin na Ibadan a kokarin matukin jiragin na sauka da misalin karfe 7:21 na yamma.
Wata majiya ta tabbatar da cewa matukin jirgin ya shirya sauka a filin jiragin tsaf gabanin faruwar lamarin, majiyar ta ce duk mutanen da ke cikin jirgin da ma’aikatan jirgin, an fito da su daga jiragin cikin koshin lafiya sai dai jiragin ya samu matsala don ya lalace.