Kamfanin AVIC mai kirar jiragen sama dake kasar Sin, ya ce jirginsa mai saukar ungulu samfurin AC313A da ya kera, ya kammala gwajin tashi da sauka a yanayi na hunturu, inda ya karkare gwaji a filin saukar jiragen sama na birnin Mohe na arewacin kasar.
Jirgin samfurin AC313A mai nauyin tan 13, na iya daukar fararen hula da dama, an kuma tsara shi ta yadda zai jure yanayi daban daban, a kuma yi amfani da shi a ayyukan gaggawa na ceto.
Bayan kammala gwaje-gwaje a yanayi na hunturu da jirgin na kamfanin AVIC ya yi, kamfanin ya ce zai sake gudanar da karin gwaje-gwaje da jirage 2 samfurin na AC313A, domin samar da takardun ingancin aiki, kafin fara aiki da samfurin jirgin nan gaba a ayyukan kasuwanci. (Saminu Alhassan)