Babban jirgin saman fasinja samfurin C919 da kasar Sin ta kera da kanta, ya karbi takardar shaidar kara kera shi ranar Talata, matakin dake nufin ana iya kara kera jirgin saman da yawa
Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin (COMAC), wanda ya kera jirgin na C919, ya karbi takardar shaidar ce daga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman kasar Sin (CAAC) dake yankin gabashin kasar.
A shekarar 2017 ne dai, jirgin saman ya kammala gwajin tashinsa na farko cikin nasara, ya kuma samu irin wannan takardar shaida a karshen watan Satumba, abin da ke nuni da cewa, tsarin na C919, ya dace da mizanin tashi da kuma ka’idoji na muhalli.
A watan Maris din wannan shekara ce, kamfanin jiragen sama na China Eastern Airlines (CEA), ya sanya hannu kan kwangilar sayen jiragen na C919 guda 5, abin ke zama kasuwancin farko na jirgin.
Sakataren hukumar CEA Wang Jian, ya bayyana cewa, ana sa ran mikawa kamfanin na CEA jirgin farko a watan Disamba, za kuma a bayar da ragowar jiragen da aka yi oda a cikin shekara 1 ko biyu masu zuwa, bisa tsarin samar da jiragen.
Ana kuma sa ran kamfanin CEA, zai fara harkokin zirga-zirga da jirgin a cikin watanni 6 na farkon shekarar 2023.(Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp