Jirgin kasa na CR450, wanda a duniya ake daukarsa a matsayin jirgi mai amfani da lantarki mafi saurin gudu a duniya (EMU), a halin yanzu ya fara zirga-zirgar gwaji domin tantancewa a layin dogo na jirgi mai falfala gudu na Shanghai zuwa Chongqing zuwa Chengdu.
An yi wa CR450 tsarin da za a ci gaba da inganta shi, da samun kwakkwaran gwaji tun daga lokacin da aka fitar da samfurinsa a karshen shekarar da ta gabata. Bayan samun nasarar cimma dukkan ma’aunai na aiki, ciki har da falfala gudun da ya kai kilomita 450 a cikin sa’a guda, a yanzu kuma wajibi ne ya zama ya yi gwajin gudanar da zirga-zirgar da ta kai adadin kilomita 600,000 cikin nasara kafin a kai ga fara jigilar fasinjoji da shi.
Wanda aka kaddamar da muhimmin shirin samar da shi a cikin 2021, tuni aikin kera jirgin na CR450 ya samar da sakamako mai ban mamaki. Haka nan, tun tuni samfurinsa ya kafa sabon tarihi a duniya a karkashin lokacin gwaji, ciki har da gudun kilomita 453 a cikin sa’a guda, har ma ya kara da wani gudun da saurinsa ya kai kusan kilomita 896 cikin sa’a daya, wanda hakan ya kara tabbatar da ci gaba da jagorancin kasar Sin a duniya a fannin fasahar kera jirgin kasa mai matukar falfala gudu. (Mai fassara: Yahuza)














