Jiya Lahadi 4 ga wata, jirgin kasa na dakon kaya na Madrid zuwa Yiwu, ya tashi daga birnin Yiwu na lardin Zhejiang dake kudancin kasar Sin, domin zuwa birnin Erenhot na yankin Mongolia ta gida, inda daga baya zai wuce birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha, kuma sau 1506 ke nan jirgin kasan na Madrid-Yiwu yake zirga zirga tsakanin kasar Sin da nahiyar Turai, kafin hakan, ya yi zirga zirga sau 500 a shekarar 2019, da kuma sau 1000 a shekarar 2021.
Hakika a shekarar bana, adadin kayayyakin da ake jigilar su ta jirgin kasan, da karuwar dawowar jirgin kasan daga Turai sun kai matsayin koli a tarihi, kuma ya zuwa ranar 4 ga wannan wata, adadin manyan akwatunan dakon kayayyakin da jirgin ya yi jigilar su tsakanin kasar Sin da Turai ya kai dubu 124, adadin da ya karu da kaso 26 bisa dari, in an kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
A ciki, adadin dawowar jirgin kasan na dakon kaya daga Turai zuwa kasar Sin ya karu da kaso 135.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana adadin darajar kayayakin da aka yi cinikin su ta jirgin kasan Madrid-Yiwu tsakanin watan Janairu zuwa watan Oktoban shekarar bana wato 2022 ya kai kudin Sin yuan biliyan 18.63. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)