Rahotanni sun bayyana cewa, wani harin da sojojin saman Nijeriya suka kai a kauyen Sabon Gida da ke gundumar Fatika a karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, sun kashe wata mata mai juna biyu da wasu matasa biyu. Hakan ya faru ne yayin da jirgin ya fatattaki ‘yan bindigar a wani daji dake kusa da kauyen inda suka arce cikin kauyen.
Daily trust ta ta samu cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 5 na yamma.
Wadanda lamarin ya rutsa da su ‘yan gida daya ne sannan kuma wasu mutanen kauyen kimanin biyar sun samu raunuka.
Wani shugaba ne a yankin, Hamisu Kurau ya tabbatar wa Daily Trust da faruwar lamarin ta wayar tarho.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp