Bisa tsarin tashi da sauka a matakin gwajin aiki da aka tsara zai gudanar, har na tsawon sa’o’i 100, jirgin saman fasinja kirar kasar Sin samfurin C919, ya yi tashin farko a cikin sabuwar shekarar Zomo, bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin.
Jirgin mallakin kamfanin China Eastern Airlines, mai lamba MU7817, ya tashi daga filin jirgin saman Hongqiao dake birnin Shanghai, inda ya sauka a filin jirgin saman Changbei dake birnin Nanchang na lardin Jiangxi dake gabashin kasar ta Sin, da misalin karfe 10:30 na safiyar jiya Asabar.
Jirgin dai ya kammala zirga zirga 2 tsakanin Shanghai da Nanchang, inda a lokutan aka gwada yanayin shigar fasinjoji, da aikin matuka jirgin, da kuma tsarin lura da lafiyarsa.
A cewar daraktan cibiyar ba da umarni ta jiragen sama a hukumar ta CEA dake lardin Jiangxi Wu Jinjun, bayan kammala sa’o’in 100, hukumar lura da sufurin jiragen sama ta Sin ko CAAC, za ta gudanar da wasu gwaje-gwaje da tantancewa, domin tabbatar da ko kamfanin na China Eastern Airlines na da kwarewar amfani da jirgin samfurin C919. Daga nan ne kuma CAAC za ta baiwa hukumar CEA lasisin fara safarar fasinjoji da jirgin a lokacin da ya dace. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp