Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na China Eastern Airlines ya bayyana a yau Litinin cewa, babban jirgin saman fasinja C919 kirar kasar Sin ya fara jigilar fasinjoji a kan sabuwar hanya da ta hada birnin Beijing da birnin Xi’an, babban birnin lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin.
Jirgin mai lamba MU2113 dauke da fasinjoji 139 ya taso daga filin jirgin saman kasa da kasa na Xi’an Xianyang da karfe 4 na yamma zuwa birnin Beijing, wanda ke nuna alamar kaddamar da hanyar kasuwanci ta yau da kullum ta biyar ta jirgin na C919.
Jirgin yana aiki a kowace rana, kana jirgin da ke komawa yana tashi daga Beijing da karfe 8 na dare. Kuma tsawon lokacin tafiyar jirgin yana kusan sa’o’i 2.5.
Jirgin na C919 ya kammala tashinsa na farko na jigilar fasinja a watan Mayun shekarar 2023, kuma tun daga lokacin ya ci gaba da gudanar da zirga-zirga tsakanin Shanghai da Chengdu, babban birnin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin.
Ya zuwa ranar Asabar, jirgin na C919 ya kammala jigilar fasinja sau 3,133, wanda ya ba da hidima ga fasinjoji kusan 420,000. (Yahaya)