Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata rahoton da wasu kafafen yada labarai suka wallafa cewa, wasu ‘yan ta’adda sun kai hari ta sama a jirgi mai saukar Angulu (Helicopter).
A cewar Gwamnatin, Jirgi mai saukar Angulu, na Sojin sama ne (NAF) da yakai Dakarun Soji suka yi artabu da ‘yan bindigar bayan sun kai hari a wasu kauyuka inda suka hallaka mutum 32 a karamar hukumar Kajuru, Kaduna.
Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumu’a.
Aruwan, ya ce “Gwamnatin jihar Kaduna ta samu rahoto daga Jami’an tsaro cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan Dogon Noma, Ungwan Sarki da Ungwan Maikori da ke karamar hukumar Kajuru a ranar Lahadin da ta gabata.
“Gwamnatin jihar Kaduna na mika ta’aziyyarta ga iyaye da ‘yan uwan wadan ‘yan bindigar suka hallaka bayan kone gidajen Jama’a da barnata dukiyoyinsu.”
Wadanda lamarin ya afka da su, sun hada da Ahmadu Musa, Audu Dandaura, Akilu Laya, David Wasika, Hajatu Buhari, Nashon Buhari Iliya Yaki, Javan Mairabo, Jackson Adamu da kuma Nasco Victor.
Sauran sune, Dutse Gwamna: Joshua Amadi, Gona Isah, Douglas Yakubu, Phineas Joel, Tanimu Umaru, Abody Iliy, Wanzami Halidu, Dogo Aweh, Sunday Shittu, Rejoice Audu, Jedidiah Ayawa Jinkai Pius, Rebecca Ayafa, Ishaya John, Audu Danladi, Jibo Sule, Yakubu Garba and Williams Danbaba.Maikasa Kufana, Augustine Bahago da kuma Mamiya Maikori.
.