Sashen kula da mambobi da sassan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya sanar a yau Jumma’a cewa, ya zuwa karshen shekarar 2022, JKS tana da mambobi miliyan 98.04.
A cewar alkaluman da sashen ya fitar, gabanin bikin cika shekaru 102 da kafuwar jam’iyyar a ranar 1 ga watan Yuli, adadin ya karu da kusan miliyan 1.33, kwatankwacin kashi 1.4 cikin 100 a shekarar 2021. (Ibrahim Yaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp