A cewar babban taron ayyukan raya tattalin arziki na shekara-shekara na kasar Sin da aka gudanar a makon da ya gabata, kasar Sin ta kara inganta manufofinta a bana, don tinkarar tasirin abubuwan da suka wuce yadda ake tsammani da kiyaye zaman lafiyar tattalin arziki da zamantakewar al’umma baki daya, wanda hakan ya kasance wata nasara mai wahalar gaske, bisa ga tsarin da aka tsara.
Babbar kasuwa, da ingantaccen ci gaban tattalin arziki da inganta yanayin kasuwanci, ya sa dimbin al’ummomin kasa da kasa suna yin tururuwa zuwa kasuwannin kasar Sin, tare da ninka ayyukansu da kara zuba jari, duk da yadda yanayin zuba jari ke ciki a duniya.
Alkaluman hukuma sun nuna cewa, a cikin watanni 10 na farkon wannan shekara, jarin kai tsaye da aka zuba a babban yankin kasar Sin ya karu da kaso 14.4 bisa 100 kan makamancin lokaci na shekarar da ta gabata, zuwa yuan triliyan 1.09.
Bangaren masana’antun fasaha, ya ba da rahoton samun ci gaba mai armashi, inda jarin kai tsaye da aka zuba a fannin, ya karu da kashi 57.2 cikin 100 bisa makamancin wannan lokacin.
Bugu da kari, cinikayyar ketare na kasar ya ci gaba da habaka. Babbar hukumar kwastam ta bayyana cewa, a tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba, cinikin kayayyakin ketare na kasar, ya karu da kaso 8.6 bisa dari kan makamancin lokacin shekarar da ta gabata zuwa Yuan triliyan 38.34.
A wani mataki na daidaita tsarin masana’antu a duniya, birane da dama na kasar Sin, sun fadada ayyukan sufuri da kaddamar da sabbin hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama, da na ruwa kai tsaye, don saukaka zirga-zirgar mutane da kayayyaki ta kan iyaka, ta yadda za a karfafa cinikayyar kasa da kasa da farfadowar harkoki a duniya.
Kasar Sin ta taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyaki a duniya ta hanyar karfafa juriyar masana’antu da samar da kayayyaki. (Ibrahim)