Gidauniyar masana kan tsarin zaman lafiya (PeacePro) ta yi Allah wadai da kiran da kungiyar Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta yi wa kungiyar ECOWAS kan amfani da karfin soji wajen tabbatar da Dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar.
Ta ce shawarar da USIP ta bayar na amfani da karfin soji kan sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar, ta yi watsi da duk wasu sanannun dabarun samar da zaman lafiya da za iya samar da matsaya mai kyau da za ta kawar da rikici.
Gidauniyar a cikin wata sanarwa da babban daraktanta, Mista Abdulrazaq Hamzat, ya fitar, ta ce ta karanta sakon USIP cikin bacin rai, wacce shugaban kungiyar, Chris Kwaja ya rattabawa hannu, inda ta bukaci ECOWAS da ta yi amfani da karfin soji wajen shawo kan al’amura a Jamhuriyar Nijar.
Gidauniyar ta ce, wasu muradun kasashen ketare da suka hada da USIP sun bukaci kungiyar ECOWAS da ta dauki matakin soji kan Jamhuriyar Nijar, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a baya-bayan nan, lamarin da ka iya jefa yankin yammacin Afirka cikin mawuyacin hali na rashin tsaro da take hakin bil adama da kuma rashin zaman lafiya.
Ta ce, duk da cewa yana da matukar muhimmanci a maido da Dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar, amma amfani da karfin soji ba zai haifar da sakamako mai kyau ba a yankin.
“Dimokradiyya ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati, amma dimokuradiyya da aka kafa ta hanyar karfin soji ba za ta iya samar da sakamakon da ake so ba,” in ji ta.