Gwamnonin Jam’iyyar adawa ta PDP sun shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki da su yi murabus daga mulkin kasar kan halin da kasar nan ke ciki matukar ba za su iya samar da mafita mai dorewa ba.
Gwamnonin sun ce, duk halin da ‘yan Nijeriya ke ciki ya rataya ne akan Shugaba Tinubu, a matsayinsa na shugaban zartarwa na Nijeriya, shugaban kasa kuma kwamandan rundunar sojin kasa, kuma jagoran Nijeriya.
- Masu Sayar Da Lemun Roba Sun Koka Kan Rashin Ciniki Saboda Tashin Farashin Kaya
- ‘Yansandan Tekun Kasar Sin Sun Kori Jirgin Ruwan Kasar Philippines Da Ya Yi Kutse Cikin Yankin Ruwan Tekun Dake Kewaye Da Tsibirin Huangyan
Gwamnonin a karkashin inuwar kungiyar gwamnonin PDP (PDP-GF) sun ce, wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke ciki ba batun kabilanci ko addini ko jam’iyya ba ce, inda suka ce APC ta nemi mulki ne domin ta magance matsalolin Nijeriya ba don ta kara ta’azzara su ba ko kuma su koma zargi, ko amfani da farfaganda ba don rikitar da asalin ainihin halin da ‘yan kasa ke ciki.
Kungiyar (PDP-GF) ta yi wannan sabon kiran ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktanta, Hon. CID Maduabum, a ranar Asabar a matsayin martani ga ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, wanda ya caccaki gwamnonin jam’iyyar PDP kan yadda tun farko suka kwatanta tattalin arzikin Nijeriya da Venezuela kan halin da kasar ke ciki.