A ranar 10 ga watan Nuwamba, an gudanar da kade-kade na tunawa da cika shekaru 50 da ziyarar kungiyar kade-kaden Symphony ta Philadelphia a kasar Sin, a gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin, tun daga shekarar 1973, kungiyar ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen kara fahimtar juna da abokantaka a tsakanin Sin da Amurka.
A shekara ta 1973, kungiyar kade-kaden Symphony ta Philadelphia ta ziyarci kasar Sin a karon farko, kuma ta zama “wakiliyar al’adu” wadda ta karfafa dangantakar Sin da Amurka a tarihi. Tun bayan wannan lokacin, kungiyar ta ziyarci kasar Sin har sau 12, ba wai kawai ta shaida gagarumin sauye-sauye a fannin kade-kade na kasar Sin ba, har ma ta karfafa abokantaka a tsakanin Sin da Amurka.
- Kwamitin Sulhun MDD Ya Kira Taron Gaggawa Kan Yanayin Da Palastinu Da Isra’ila Ke Ciki
- Kasar Sin Na Adawa Da Duk Wani Abu Da Zai Yi Illa Ga Fararen Hula Da Keta Dokokin Kasa Da Kasa
Dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ta kara tabarbarewa matuka tun bayan da Amurka bisa son ra’ayinta ta kaddamar da yakin cinikayya da kasar Sin a shekarar 2018, lamarin da ya jawo matukar damuwa daga al’ummomin duniya game da “sabon yakin cacar baki”.
A watan Nuwamban shekarar 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden a birnin Bali na kasar Indonesiya, inda shugabannin kasashen biyu suka yi tattaunawa mai zurfi ta sahihanci, bisa manyan tsare-tsare kan manyan batutuwan da suka shafi dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da fatan samun zaman lafiya da ci gaban duniya.
A ‘yan watannin baya-bayan nan, manyan jami’an gwamnatin Amurka sun ziyarci kasar Sin sau da dama, lamarin da ya haifar da karuwar huldar da ke tsakanin sassan biyu, da kuma karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu sannu a hankali.
Farfado da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, ya kuma sa kaimi ga maido da mu’amalar jama’a tsakanin Sin da Amurka, tare da taka muhimmiyar rawa wajen daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata.
A daren bikin tunawa da cika shekaru 50 da ziyarar kungiyar kade-kaden Symphony ta Philadelphia a kasar Sin, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatar da aka yi masa, shugaba Xi Jinping zai tafi birnin San Francisco na kasar Amurka, don gudanar da taron gudanar da shawarwari tare da shugaban Amurka, da kuma halartar kwarya-kwaryar taron koli karo na 30 na kungiyar APEC, ke nan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ta shiga “Lokacin San Francisco” a hukumance.
Hakan dai ya samu ne bayan da kasashen biyu suka cimma matsaya kan “Komawa Bali”, amma cimma manufar “Lokacin San Francisco” ba za ta zo da sauki ba.
Kamar yadda wasu masana suka yi nuni da cewa, sabuwar huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka ta cewa, duniya ba ta zama karkashin ikon Amurka kadai ba, yayin da ake fuskantar karuwar tasirin da kasar Sin ke da shi a duniya, dole ne Amurka ta nemi sabbin hanyoyin yin zaman tare da kasar Sin.
Jama’a da dama na fatan dangantakar kasar Sin da Amurka za ta iya fitowa daga cikin “yanayi mai sanyi” a dalilin bikin kade-kade na tunawa da cika shekaru 50 da ziyarar kungiyar kade-kaden Symphony ta Philadelphia a kasar Sin, ya kamata kasashen biyu su kiyaye wannan lokaci na annashuwa da aka samu ba cikin sauki ba, da yin aiki tare don samun ci gaba tare, ta hakan za a guji sake samun tabarebarewar dangantakar dake tsakaninsu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)