Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.
Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.
Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.
Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta hanyar yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima ya kasance wani zabi mai inganci, wanda ya cancanci a kula da shi a kasar sosai.