A yau Lahadi, kafar CMG ta gudanar da taron manema labarai, inda ta nuna wasu sassa na kirkire-kirkire, wadanda za a yi amfani da su yayin bikin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta Sin ta bana, wadda kafar za ta watsa wa duniya, da kuma jerin masu gabatar da shirye-shirye da yadda aka kayata dandalolin gudanar da su.
Rahotanni na cewa, yayin shagalin bikin da za a gudanar, tun bayan da aka sanya bikin bazara na sabuwar shekarar kasar Sin cikin jerin al’adu da ba na kayayyaki ba da aka gada daga kaka da kakanni, a wannan karo an hade karin sassan al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba cikin bikin, kana za a yi amfani da bikin a matsayin gadar hade manufofin yayata musayar al’adun gargajiya na kasa da kasa, da yaukaka koyi da juna tsakanin mabanbantan wayewar kai.
Kari kan hakan, yayin shagalin bikin bazara na bana, a karon farko, za a kaddamar da samfurin bikin na ajin masu larurar gani, da masu larurar ji. (Saminu Alhassan)