Kafofin watsa labaru na kasashen Afirka da dama na ci gaba da mai da hankali a kan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC a takaice, inda suka bayyana cewa, taron ya nuna yadda za a zurfafa da ma kara azama kan hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.
Jaridar The New Times ta kasar Rwanda ta rubuta cewa, sanarwar da aka zartas da ita a wajen taron, ta karfafa ra’ayin bai daya da kasashen Afirka da Sin suka samu kan manyan batutuwa, da kuma tsara hanyar aiwatar da hadin gwiwa mai inganci a tsakanin Afirka da Sin a nan gaba.
- Gwamnatin Tarayya Ta Fara Sayar Da Buhun Shinkafa Kan Dubu 30
- An Kwaso ‘Yan Nijeriya 167 Da Suka Makale A Libya – NEMA
Kafar watsa labarai ta kasar Ghana “Ghana Web” ta wallafa sharhi mai taken “Taron kolin Beijing na FOCAC: Sabon zamani na hadin gwiwar Sin da Afirka” jiya Alhamis cewa, taron kolin Beijing na FOCAC, zai tabbatar da makomar ci gaban dangantakar Sin da kasashen Afirka a nan gaba, da kuma bude sabbin hanyoyin yin hadin gwiwa a fannonin da suka shafi cinikayya, zuba jari, fasahohi da dai sauransu.
Kafar yada labarai ta Independent Media ta kasar Afirka ta kudu ya rubuta sharhi mai taken “Hadin gwiwar tattalin arziki shi ne hanyar da ta hada Afirka da Sin”, inda aka bayyana cewa, matakan hadin gwiwa da aka dauka karkashin tsarin FOCAC sun nuna cewa, dandalin sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, zai iya samar da sakamako mai inganci. (Bilkisu Xin)