Hukumar UNESCO ta yanke shawarar shigar da Bikin Bazara wanda Sinawa ke gudanar da shirye-shirye daban-daban don murnarsa, cikin jerin sunayen al’adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na UNESCO, a ran 4 ga watan Disamban. Shagalin murnar Bikin Bazara da babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya kan gabatar a kowace shekara, ya zama wata al’ada mafi muhimmanci ga Sinawa a wannan muhimmin lokaci, har kundin bajimta na Guinness ya ayyana shi a matsayin shirin talibijin mafi samun masu kallo a duniya.
Kwanan baya, CMG ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kafofin yada labarai na kasashen Peru da Brazil da Nepal da dai sauransu, don gabatar da labarai dangane da wannan gagarumin biki dake yayata al’adun gargajiyar Sinawa da kara cudanyar al’adu tsakaninsu. Sassan Turancin Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da harshen Rasha na gidan telibijin na kasa da kasa na kasar Sin dake karkashin CMG wato CGTN, da kuma sauran sassan masu aiki da harsuna 81, za su yi hadin gwiwa da kafofin yada labarai fiye da 2600 na sassa daban daban na duniya, ciki har da na kasashen Amurka da Canada da Birtaniya da Faransa da Jamus da Austriliya da Peru da Brazil da Afirka ta kudu da Kenya, wajen yada shagalin murnar Bikin Bazara na shekarar 2025, wato shekarar Maciji bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin kai tsaye da gabatar da labarai dangane da shagalin. (Amina Xu)