A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe.
Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga a dama da ita, kuma za ta kasance mai bayar da shawarwari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Da yake tsokaci game da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, Lou ya ce, daukar matakin da Amurka ta yi bisa radin kai ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya, kuma ya kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya. Kakakin ya kara da cewa, kamata ya yi Amurka ta yi aiki tare da kasar Sin kuma su fahimci juna don warware takaddamar cinikayya ta hanyar yin shawarwari bisa daidaici.
Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana matukar martaba dangantakarta da kasashen Turai, kuma sassan biyu abokan hulda ne dake ba da gudummawa ga samun nasarar juna. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp