An rufe taron ministocin kula da muhalli da yanayi na kasashen kungiyar G20 a kasar Indiya a kwanakin baya. Wasu kafofin watsa labaru na yammacin duniya sun tsamo ra’ayoyin wasu mutane a gun taron, wadanda ke cewa matsayin Sin ya kawo cikas ga cimma daidaito a fannonin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, da dakatar da amfani da makamashin da ba a sake amfani da shi ba, da kara amfani da makamashin da ake iya sabuntawa da saransu.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, labarin ba shi da tushe ko kadan. A ranar 28 ga watan Yuli, an cimma yarjejeniyar samun daidaito da samar da bayanin da ya takaita batutuwan da aka tattauna yayin taron, hakan ya shaida cewa, an samu sakamako mai kyau. Amma sakamakon tabo batun siyasa da wasu kasashe suka yi, ba a cimma sanarwar taron ta karshe ba, kuma Sin ta yi bakin ciki da hakan.
Kakakin ya bayyana cewa, Sin ta sa kaimi ga tinkarar matsalar yanayin duniya, kana ta yi kokarin samar da gudummawa da goyon baya ga sauran kasashe masu tasowa, haka kuma ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa kan tinkarar sauyin yanayi har guda 43 tare da kasashe masu tasowa 38, da horar da kwararru da jami’ai a wannan fanni ga kasashe masu tasowa fiye da 120. (Zainab)