Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin ya yi Allah wadai da kasar Australia bisa yadda ta zargi kasar Sin da yin atisayen soja bisa doka a tekun dake kusa da kasar ta Australia.
Kakakin, Wu Qian ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin kafofin watsa labaru game da zargin na Australia cewa jiragen ruwan yaki uku na kasar Sin sun yi atisayen soja a tekun dake kusa da kasar Australia.
Wu Qian ya bayyana cewa, zargin da kasar Australia ta yi ba shi da tushe balle makama, domin yankin tekun da jiragen ruwan yakin na kasar Sin suka yi atisayen soja yana can nesa da layin teku na kasar Australia, kuma yanki ne da ba ya cikin mallakar wata kasa. Kakakin ya kara da cewa, kafin lokacin, sai da kasar Sin ta ba da sanarwa sau da dama a kan gudanar da atisayen, sai dai kuma abin mamaki, bayan da jiragen ruwan yakin kasar suka harba boma-bomai zuwa tekun, sai Australiya ta yi zargin.
Ya ce, Sin ta gudanar da ayyukan atisayen bisa dokokin kasa da kasa da ka’idojin zirga-zirga na kasa da kasa, wadanda ba za su kawo illa ga tsaron zirga-zirgar jiragen sama ba. Kuma kasar ta Australia ta san lamarin, amma kuma ta zargi kasar Sin da abin da ba shi da tushe balle makama, kuma Sin tana nuna rashin jin dadinta game da batun. (Zainab Zhang)