A yau ne, a taron manema labarai, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, babban kanar Wu Qian, ya gabatar da yadda aka gudanar da atisayen hadin gwiwa na sojojin Sin da Tanzaniya da Mozambique, a kwanakin baya.
Wu Qian ya ce daga ranar 29 ga watan Yuli zuwa ta 11 ga watan Agusta, sojojin kasar Sin sun gudanar da atisayen hadin gwiwa na “Zaman lafiya da hadin kai na 2024” tare da sojojin Tanzaniya da Mozambique. Kuma kasar Sin ta aike da bataliyan sojojin kasa da jiragen ruwan yaki guda uku don halartar atisayen, kana ta yi amfani da jiragen sama na Y-20 kirar Sin wajen aiwatar da rawan daji. Yayin da sama da dakaru 1,100 da jiragen ruwa shida na sojojin Tanzaniya da Mozambique ne suka halarci atisayen. Taken wannan atisayen shi ne a hada kai don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, tare da gudanar da cikakken aiki a babban matakin yaki.
Wu Qian ya kara da cewa, sojojin kasar Sin na son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da sojojin kasashen Afirka don ci gaba da sada zumuncin gargajiya, da zurfafa hadin gwiwarsu, da kara ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Mai fassara: Yahaya)