Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana yau Laraba a gun taron manema labarai da aka saba yi cewa, abin da duniya ta fi bukata shi ne hadin kai, kuma ya kamata a kiyaye rarrabuwar kawuna. Duk wani matakin da zai cutar da wata kasa, da duk wani tunanin nuna kiyayya tsakanin bangarori, da duk wani girman kai ba za su haifar da kyakkyawan sakamako a karshe ba.
Wang Wenbin ya kara da cewa, kamata ya yi mu yi kira da samun dunkulewar tattalin arzikin duniya da zai amfanar da kowa da kowa, da yin adawa da wargajewar tattalin arzikin duniya, da tabbatar da tsaro, da kin duk wani nau’i na kin jin ra’ayin bangarori daban daban da ba da kariya kan ciniki, da inganta samun daidaito da damammaki da ka’idoji cikin adalci tsakanin kasa da kasa, da kiyaye hakkoki na ci gaban dukkan kasashe, da inganta ci gaba da wadata tare. (Yahaya)