Mutane daga bangarori daban daban na Taiwan sun bayyana matukar damuwa game da kalamai na baya bayan nan da jagoran yankin Taiwan Lai Ching-te ya furta, suna gargadin cewa kalaman za su iya ta’azzara zaman dardar da kawo cikas ga mu’amala tsakanin babban yankin Sin da Taiwan din.
Yayin wani taron manema labarai a ranar Alhamis, Lai Ching-te ya bayyana babban yankin kasar Sin a matsayin ’yar adawa, tare da gabatar da wasu dabaru 17 na yaki da barazanar da tsibirin ke fuskanta.
- Yadda Sulhun Shugabannin Al’umma Da ‘Yan Bindiga Ke Haifar Da Da Mai Ido A Katsina
- Sin Ba Za Ta Taba Amincewa Da Ayyukan ’Yan Aware Ba
Wani sharhi da jaridar The United Daily News dake Taipei ta wallafa, ya yi gargadin yunkurin Lai na iya jefa Taiwan karkashin dokar soja, da kuma mayar da hannun agogo baya don gane da mu’amalar da ake yi tsakanin babban yankin Sin da tsibirin.
Hung Hsiu-chu, tsohuwar shugabar jam’iyyar Chinese Kuomintang, ta bayyana manufofin Lai a matsayin masu iyaka da dokar soji, tana mai zarginsa da manakisar siyasa.
Su ma shugabannin ’yan kasuwa sun bayyana damuwarsu, inda Jivan Huang, shugaban wani rukunin masana’atu ya yi gargadin cewa, daukaka wani ra’ayi sama da tunani da hankali, zai takaita yanayin tafiyar tattalin arzikin Taiwan. Yana mai cewa babban yankin kasar Sin shi ne wuri mafi muhimminci ga Taiwan ta fuskar zuba jari da samun rarar cinikayya. Ya kara da cewa, kalaman na Lai ka iya rage karfin takarar da kamfanonin Taiwan ke da shi.
A bangaren yawon bude ido kuwa, Ringo Lee, shugaban kungiyar masu shirya tafiye-tafiye, ya koka cewa, hukumomin jam’iyyar DPP na nuna wariya ga wadanda ke son hulda da babban yankin kasar Sin, kuma tilas hakan zai yi mummunan tasiri kan mu’amala ta yau da kullum dake tsakanin bangarorin biyu. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp