• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kallon Kankara Da Wasa Da Dusarta Na Matukar Kayatarwa A Birnin Harbin Na Kasar Sin

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Kankara

•Wasan hockey kan kankara

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Birnin Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin, yana da dadadden tarihi, inda yau shekaru dubu 22 da suka gabata ke nan da ’yan Adam suka fara rayuwa a wurin.

Sinawa kan kira birnin Harbin da sunan “birnin kankara”, saboda matsakaicin zafin yanayi a birnin ya kan yi kasa da digiri sifiri har tsawon watanni 5 a kowace shekara. Sanyi ya kawo wa ’yan birnin basira, a lokacin hunturu su kan yi wa birnin na Harbin ado da kankara da dusar kankara, har ma Harbin ya zama tamkar wani kyakkyawan wuri da aka iya gani a cikin hikaya kawai.

  • Babbar Masana’antar Manyan Bayanai Ta Kasar Sin Ta Inganta Matuka

Birnin Harbin yana yankin kusurwar sama a doron kasa, zafin yanayi a wurin ya yi kasa da digiri sama da 20 a karkashin sifiri a farkon lokacin hunturu. Sanyi ya karfafa kyan ganin Harbin sosai, Harbin kuwa ta samar da al’adunta na musamman mai launin fari, ta shirya bikin al’adu na kankara da dusar kankara, wato bikin kankara da dusar kankara na duniya. Bikin kankara da dusar kankara na kasa da kasa na Harbin, shi ne bikin kasa da kasa na farko da kasar Sin ta shirya dangane da wasannin kankara da dusar kankara.

Tun daga shekara ta 1985 da ta gabata, wannan kasaitaccen biki ya kan karbi baki daga wurare daban daban a kowace ranar 5 ga watan Janairu, wanda kuma a kan dauki wata guda ana gudanar da shi. Bikin kankara da dusar kankara na kasa da kasa na Harbin da irinsa na birnin Sapporo na kasar Japan, da na birnin Quebec na kasar Canada, da na birnin Oslo na kasar Norway, manyan bukukuwa ne na kankara da dusar kankara guda 4 a duniya.
An yi kwanaki sama da 100 ana yin wannan bikin kankara da dusar kankara.

Kankara
•Daukar hoto da kankara

A lokacin nan, mutum-mutumin da aka yi da kankara sun tsaya a tituna da unguwoyin birnin Harbin. Ban da wannan kuma, mutane su kan sa kayayyakin launuka ko kuma fitilu masu launuka a cikin kankara, ta haka mutum-mutumin da aka yi da kankara za su kasance a bayyane, kuma suna yin haske masu launuka iri daban daban da dare.

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Yanzu za mu gaya muku yadda aka sassaka wadannan mutum-mutumi da kankara. Bayan shigar lokacin hunturu, kogin Songhuajiang dake kewayen birnin Harbin ya zama wani babban fili mai kankara, har ma idan kankara na da tauri, mota na iya gudu a kansa. ’Yan birnin Harbin masu fasaha sun haka kankara daga kogin, sun yi amfani da injin yanka na musamman sun yayyanka kankara zuwa siffofi daban daban, daga baya, sun sassaka mutum-mutumi da wadannan kankara.

Idan ba ku gamsu da mutum-mutumin da ke kan tituna da wuraren shakatawa ba, to, wurin shakatawa dake gabar arewa ta kogin Songhuajiang wuri ne dake iya biyan bukatunku. Fadinsa ya kai murabba’in mita 400,000 ko fiye, wanda wurin shakatawa ne mafi girma a birnin Harbin, inda ake nuna kayayyakin kankara da dusar kankara. A cikin wannan wurin shakatawa, hasumiyoyi da dakuna da farfajiya da kuma manyan farfajiya, dukansu an yi su ne da kankara. Mutane na iya sa kafa kan benayen kankara a maimakon kallonsu kawai.

Kankara
Birni mai kankara

Ban da mutum-mutumin da aka yi da kankara, an sassaka mutum-mutumi da dusar kankara a Harbin. Tsibiri mai suna “Duniyar Rana” da ke arewacin gabar kogin Songhuajian wuri ne mai kyau wajen kallon mutum-mutumin da aka yi da dusar kankara. Saboda iska na da tsabta, kuma dusar kankara na da kyau a nan, shi ya sa hukumar Harbin ta kan shirya bikin baje koli na mutum-mutumin da aka yi da dusar kankara sau daya a ko wace shekara.

Ba kayayyakin fasaha ’yan birnin Harbin suka samar ta amfani da kankara da dusar kankara kawai ba, har ma sun gina na’urorin shakatawa da su. A cikin wurin shakatawa na Zhaolin na Harbin, an gina wata babbar hanyar fita daga daki mai wahalar ganewa da kankara, wadda tsawonta ya kai misalin mita 60, tilas ne mutane su mai da hankali sosai, kada santsi ya kwashe su a lokacin da suke neman fita waje a cikin wannan babbar hanyar fita daga daki mai wahalar ganewa. Sa’an nan kuma, kada su manta da yin wasa da sululu mai tsawon mita 10 ko fiye. A lokacin da wani ya gangaro daga kansa cikin sauri kan hanyar kankara, zai ji iska ta bugi kunnensa.

Idan kana son kara jin dadin wasannin kan kankara, to, tabbas ne ka je kogin Songhuajiang. Bayan da ruwan kogin ya daskare, kogin Songhuajiang ya zama wurin shakatawa ne na halitta a birnin Harbin. Mutane na iya kallon wurare masu ni’ima dake gabobin kogin kan kekunan tafiya da karnuka suke ja a kan kankara, haka zalika kuma suna iya kallon masu kishin iyo a lokacin hunturu na iyo a cikin kogin.

Kankara
Mutum-mutumin dusar kankara a Harbin

In an tabo magana kan wasannin kan kankara, tilas ne mu tuna da wasan skiing a tsakanin duwatsu. Birnin Harbin wuri ne mai dacewa da wannan wasa. A cikin dukkan filayen wasan skiing a tsakanin duwatsu da ke wannan birni, filin wasan skiing a tsakanin duwatsu na Yabuli ya fi shahara, wanda ya fi girma a duk kasar Sin. Yana kan gaba a kasar Sin a fannonin yawan hanyoyin wasan skiing da aka shimfida da kuma tsawonsu da tsayinsu da kuma samar da sauran na’urorin wasan skiing.

Ko da yake zafin yanayi a yanzu a wajen daki ya kai digiri 20 kasa da sifiri a Harbin, amma mutane masu yawa suna jin dadin wasannin motsa jiki kan kogin da ya daskare, musamman ma wadanda suka fito daga wurare masu dumi a kudancin kasar Sin.
Ga wasu matasa daga birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, suna sha’awar yin tafiya a kan daskararren kogin Songhuajiang. Da ma ba su taba ganin kankara ba, yanzu ba sa son komawa daki, sun yi ta gwajin wasanni iri daban daban masu ban sha’awa kan kankara.

A ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2022 da ta gabata, aka kaddamar da shagalin kankara da dusar kankara tsakanin al’umma na kasar Sin karo na 9 a birnin Harbin, wanda babban taken shagalin shi ne kama sabuwar hanyar shiga sabon zamani da kuma raya wasannin kankara da dusar kankara. A cikin lokacin hunturu na farko bayan gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, wasannin kankara da dusar kankara suna bunkasa sosai a sassa daban daban na kasar Sin.

Kankara
Shagalin kankara da dusar kankara na Harbin

Wani saurayi mai suna Zhang Chupeng, wanda ke sha’awar wasan gudun dusar kankara sosai, ya bayyana mana cewa, abokansa da dangoginsa suna kara sha’awar wasan gudun dusar kankara bayan gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing. Da zarar an shiga lokacin sanyi, to jikunansu a shirye suke wajen yin wasan gudun dusar kankara. Suna son wasan gudun dusar kankara a kowace rana!

Rahotanni sun ruwaito cewa, za a gudanar da shagalin kankara da dusar kankara tsakanin al’umma na kasar Sin karo na 9 har zuwa watan Afrilun shekarar 2023 da muke ciki, inda kuma za a shirya harkokin wasannin kankara da dusar kankara 1499 tsakanin al’umma a sassa daban daban na kasar Sin.

Kankara
Wasan kwalle-kwalle a kan kankara

Masu karatu, ko kuna sha’awar irin wadannan wasannin kankara da dusar kankara? Ko kuna sha’awar kallon mutum-mutumin da aka yi da kankara da dusar kankara? Muna maraba da ku a birnin Harbin mai kankara da ma sauran wuraren kasar Sin! (Mai fassarawa: Tasallah Yuan daga CMG Hausa)


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Babbar Masana’antar Manyan Bayanai Ta Kasar Sin Ta Inganta Matuka

Next Post

Wane Shugaban Kasa Zai Gaji Kasafin Kudin Buhari Na Karshe?

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

2 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

10 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

10 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

11 months ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
Buhari

Wane Shugaban Kasa Zai Gaji Kasafin Kudin Buhari Na Karshe?

LABARAI MASU NASABA

Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

Dakarun Soji Sun Daƙile Wani Sabon Harin ISWAP A Dikwa

May 14, 2025
Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte

May 14, 2025
Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

May 14, 2025
Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.