Mata na da muhimmanci ta kowane fanni na rayuwa kuma suna bada gudunmawa mai tarin rayuwa ga rayuwa da kuma ci gaban kasa. Mata da yawa na shiga tafiyar siyasar kasar nan tun tuntuni, kuma sun taka rawa mai tarin yawa wajen tafiyar da gwamnati a fanni daban-daban.
Leadership Hausa ta cikin shirinta na ‘Twitter Space’ a kan maudin da ya shafi irin rawar da mata za su taka a siyasar 2023.
- Ziyarar Da Shugabar Tanzaniya Za Ta Kawo Sin Za Ta Bunkasa Alaka Tsakanin Kasashen Biyu Zuwa Wani Sabon Matsayi
- Kumbon Dakin Gwaji Na Mengtian Ya Hade Da Tashar Binciken Sararin Samaniya Ta Kasar Sin
A bayyana ne yake kowa ya san mata na da muhimmiyar rawa da za su bayar a zaben da ke kara karatowa na shekarar 2023.
Misalin idan aka yi duba a baya a Arewa, za a ga akwai mata irin su Hajiya Gambo Sawaba, Hajiya Aisha Maman Taraba, Hajiya Naja’atu da sauran mata masu tarin yawa da suka yi bajinta a siyasar Arewa da kasar nan baki daya.
Shigar Mata Cikin Harkokin Siyasa Na Da Alfanu
Hassana Alkali, daya daga cikin bakin da aka gayyato ce, wadda lauya ce, kuma ta yi bashin baki game da irin rawar mata a siyasar Arewa da ma kasar nan baki daya.
“Duba da bincike da aka yi a 2019 za a ga cewar maza suna cikin kaso na 84.2 na mambobin majalisar kasa, kuma shigar mata cikin harkokin siyasa na da alfanu mai tarin yawa duba da irin rawar da suke bayarwa tun daga gida.
“Duk da cewar wasu na ganin cewar shigar mata harkokin siyasa na da matsala tun daga gida za ta dinga samun kalubale cewar ita mace ce, ita mai rauni ce. Amma da za a duba akwai gudunmawa da zamu bayar a siyasar Najeriya duba da irin rawar da muke bayarwa tun daga gida zuwa ita kan ta siyasar,” kamar yadda ta bayyana.
Mata Sun Fi Jefa Kuri’a A Lokacin Zabe
Mata na daga cikin wadanda suke tsayawa kai da fata wajen jefa kuri’a a lokutan zabe, amma idan an zo rabon madafun iko sai a ga ba su samu wasu gurabe masu gwabi ba, shi ma wannan Hassana Alkali ta yi tambihi a kan lamarin.
“Kamar yadda na fada a baya ana daukar mata cewar su masu rauni ne, kuma an dauki cewar siyasa kamar iya maza ne za su iya yinta, idan mace ta fito sai a ce ba za ta iya rike mukami ba saboda tana da rauni. Kuma abun ya samu asali ne tun daga gida saboda irin rashin goyo baya da ake ba su.
“Zaka ji ana cewa me mace za ta yi da siyasa ba fanninta ba ne fannin namiji ne, ka ga tun daga gida ta fara samun kalubale. Idan ta fita waje nan ma za ta fuskanci kalubale daga wajen maza.”
Mata Da Matasa Ne Suka Fi Yin Rajistar Zabe
Ta kara da cewar mata na da muhimmanci sosai a lokutan zabe.
“Yanzu idan aka duba jadawalin da INEC ta fitar cewar mata da matasa ne mafi yawan mutanen da suka yi rajistar katin zabe, ka ga kenan cewar mata suna taka muhimmiyar rawa a lokutan zabe.
“Ina tunanin akwai bukatar fitowa don goya mata gaya don ganin ta cimma gaci don akwai tarin kalubale mai yawa.”
An Bar Mata A Baya
Shi kuwa Habib, wanda na daya daga cikin wanda suka tsinkayi shirin ya bayyana ra’ayinsa tare da goyon bayansa akan abin da Hassana ta fada game da maudin da aka tattauna.
Barista Hassana Alkali, ta buga misali da irin koma baya da mata ke samu a siyasar Arewa.
“Misali ni daga Jihar Yobe na fito, idan aka yi duba tun daga kasa muna da shugabannin kananan hukumomi, za ka ga kaf cikinsu mace daya ce kawak shugabar karamar hukuma a Yobe, sauran dun maza ne, sannan a Yobe mata da suke siyasa gaba daya kadan ne kuma ba wani kwarin gwiwa ake ba su ba.
“To irin wadannan abubuwan sai ana dubawa, shi yasa har kullum muke jan hankalin mata suke shiga harkar siyasa.
Kaso 60 Cikin 100 Na Masu Kada Kuri’a Mata Ne
“Kaso 60 na wadanda suke kada kuri’a mata ne amma basu da ra’ayin zabar zabinsu, da yawa mazajensu ne ko ‘yan uwansu ne ke tilasta musu zabar wani daban ko kuma a ba su kudi don zabar wani wanda ba zabinsu ba.
“Don haka yana da kyau mata su gane cewar juya akalar zabe na hannun mata saboda da yawan masu kada kuri’a mata ne amma da zarar an ci zabe za ka da wuya ka ji wani abu da ya shafi rayuwar mata a matsayin kudurin za a gabatar a majalisun kasar nan,” in ji Barista Alkali.
Mata Ba Su Da Juriya
KB Saje, cewa ya yi matan Arewa da ma kasar baki daya na ganin ana durkusar da su a kowane fanni na rayuwa.
“Matan na ganin akwai fifiko da ake yi a kansu a kan duk wani abu da ake yi, akwai mata manya-manya da suka yi rubuce-rubuce akan halayyar maza a siyasa tun daga siyasar kasashen ketare zuwa siyasa ta kasa-kasa.
“A Nijeriya babu wata mace da ta fito takarar siyasa aka hana ta, sai dai inda muka fito, wato al’ummarmu, al’adarmu, addininmu su suke rage musu karfi sannan su kuma ba su da juriya su zauna su yi yadda maza suke yi.
“Misali a ce idan za a yi taron siyasa kamar ja manyan ‘yan siyasa da daddare suke yin taro kamar karfe 1 ko 2 na dare suke farawa.
“Ta yaya matar da take da miji ko budurwar da ba ta yi aure ba za ta yi irin wannan taron?
“Abu na biyu kuma, duk inda ‘yan siyasa ke taro za ka ga al’umma ne ke taruwa suna kururuwa kuma za ka ga wannan taron ba wanda zai damu da kai namiji ne ko mace kowa faman ta kansa yake har su kansa manyan ‘yan takara ko da kuwa shugaban kasa ne, idan ba don jami’an tsaro ba za ka ga su kan su ‘yan siyasar ture su ake yi.”
Mata Ba Za Su Iya Jure Gwagwarmayar Siyasa Ba
KB Saje ya ce mata ba su iya jure irin dambarwar da ake yi a wajen tarukan siyasa ba.
“Su kuma mata ba za su jure irin wannan ba sai su dauka cewa ai ana nuna musu wariyar jinsi ne ko banbanci.
“Don haka a ko yaushe matakinka ne zai kai ka ga nasara, alal misali, idan ka dauki mataimakiyar gwamnan Kaduna, ta dade tana siyasa amma siyasar ta fi yinta a inda take aiki ko kuma idan an ci mulki sai a dauke ta a mata mukami, ba ta cika shiga cikin hargitsi ba.
“Ta biyu, akwai Maman Taraba ta tsaya takarar Sanata a Taraba lokacin da ta zo ba ta sha wahalar siyasa ba a zahirince, saboda me? Ta zo da kudi kuma mutane sun dan santa sannan mijinta ya yi shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan yayanta ya yi takarar gwamna a Taraba kuma ita ma tana nan lokacin da yake wannan takarar.
“Jama’a sun san ta kuma tana da ‘yan uwa, ta yi nasara a wancan lokaci a Sanata amma a matakin gwamna a Taraba sai ya kasance akwai illoli na siyasar addini da sauransu don haka ba ta yi nasara ba a zahiri, amma an je kotu.
“Matsalolin mata a ko yaushe su kan dauki abin da mutane kalilan suka fada musu, idan kina siyasa sai a ce wannan ba ta da kunya, ai ko namiji da yake siyasa wasu za su ke ce masa ‘yan siyasa makaryata ne.
“Su kuma mata idan aka fada musu haka sai su ji cewar an hada su da wani abu lalatacce ne, duk dan siyasa cewa ake yi makaryaci ne, idan mata ne a ce musu ‘yan iska ne kuma wannan ba za su taba guje masa sai dai in za su bar siyasar.
“Sannan kuma a kan same su da rauni wani lokacin,” cewar KB Saje.
Ba A Bai Mata Gudunmawar Da Ya Dace
Sani Ahmad Kazaure, daga Jami’ar Jihar Jigawa, ya ce wannan maudu’i ne mai matukar muhimmanci da ya kamata ake tattauanawa a kan su.
“Binciken da aka yi na wanda suke kada kuri’a a lokutan zabe, kashi 60 cikin 100 mata ne ke jefa kuri’a, mata su suke yin zabe sosai.
“To amma idan ta kasance bayan zabe ba a ba su dama, muhimmanci ko gudunmawar da ya kamata.
Babban Kalubalen Mata A Siyasa Shi Ne Rashin Hadin Kai
“Babban kalubalen mata a siyasa shi ne rashin hadin kai, domin idan suka hadu suka zama tsintsiya madaurinki daya suka yarda cewar idan aka bai wa wance za ta mana adalci to za su cimma gaci, to wannan hadin kan shi ne abu na farko.
Addini Da Al’Ada Na Hana Mata Rawar Da Ya Kamata
“Sannan mu nan Arewa kamar akwai addini da sauransu ba irin siyasar da muke tunanin mace ta fito a yi gwagwarmays da ita ba, misali akwai ko a Jami’a idan ka ga mace tana siyasa irin ta harkar dalibai za ka ga ana mata wani irin kallo ba ta da daraja ko ba ta da mutunci ko ba ta san darajar kanta ba.
“Ba haka bane ba, dole ne sai an cire irin wannan tunanin, irin siyasar da ya kamata a ce mata suna ciki ita ce ta ilimi da bada gudunmawa da tsayawa akan jajircewa kan an yi abin da yake daidai.
“Duk inda aka ce misali gwamnati ta yi wani abu na ba daidai ba, idan da mata za su fito su yi zanga-zanga, to wannan abun za ka ga yana da matukar tasiri sama da a ce matasa ne da manya suka fito suka yi.
“Maimakon a ce sai lokacin da barna ta faru me zai hana mata su samu wata inuwa su dinga tattaunwa su fito da wata mukala, su ce wannan matsalarmu ta mata su turawa gwamnati su ce sai an yi kaza ko sai mun samu kaza wannan zai taimaka kwarai da gaske.
“Saboda yanzu a addinance malamanmu suna hawa mambari suna maganar siyasa, limamin masallacin Juma’a ya yi, limamin masallacin sallalo biyar ya yi, mai unguwa ya yi, to me zai sa ba za a bar mata su shiga sabgar siyasa a dama da su ba?”
Kudaden Sayen Fom Takara Na Jam’iyyun Siyasa Na Kashe Muradin Mata
Wasu kuma da suka tsinkayi shirin, sun bayyana cewar irin madudan kudade da jam’iyyun siyasa ke ke laftawa wajen sayen fom din takara shi ma yana bada gudunmawa wajen hana matan shiga a dama da su, misali sai ka ga jam’iyya ta ayyana miliyan 100 ko sama da hakan a matsayin kudin da dan takara zai sayi fom din takara.
Wannan na dakile burin mata na shiga a dama da su, saboda wasu matan da yawa ba su sa wannan kudi ko hanyar samun kudin, ba ma iya matan ba har mazan da suke shiga siyasa ba su da hanyar samun wadannan makudan kudade da jam’iyyun siyasa ke sanyawa fom din takarar ‘yan siyasa.
Duk da cewar an ragewa mata kaso 75 na kudin fom da jam’iyyun siyasa suka saka, amma hakan na iya dakushe musu buri da kuma kawo barazana ga cikar burin mata na siyasa.
Dole Mata Su Nemi Kudi Don A Dama Da Su A Siyasa
KB Saje ya ce idan har mata na son a ci gaba da damawa da su a siyasa dole ne su ma su dinga nemo irin wadannan kudaden da maza ke biya wajen sayen fom din takara.
“Dole ne mata suke nemo irin wadannan kudade, domin siyasa ba ta yiwuwa a Nijeriya ba kudi, idan aka duba ko da a Amurka ne matsalar siyasarsu irin tamu ce sai da kudi ake yin nasara.
“Abu na biyu kuma dole ne sai an yi sadaukarwa, sai mutum ya bada lokacinsa sosai mutum ya karanci ya bangaren siyasar yake kuma yaya lamarin nasararka take kai da kanka ka lura da me zaka fito kuma da wa zaka fito, idan ka fito da shi wace nasara zaka yi sannan wadanne mutane kake da su, ma’ana duk abin da ka fada musu za su amince da kai su yi, to wannan zai baka nasara.
“Alal misali, Binani ta yi Sanata za ta iya fadawa mutane abin da ta yi, Maman Taraba idan ta ce za ta yi abu ta yi su, amma duk sauran matan suna da kudi, don haka idan da kudinka za ka yi nasara.
“Abu na gaba, ke a matsayinki na mace zaki fito siyasa, to ki ajiye a ranki cewa idan zaki yi takara nan da shekaru biyar masu zuwa, to tun yanzu zaki shirya ta ta zaki yi suna a wajen al’ummarki kuma sunan mai amfani sunan da zai zama za s kalle ki a matsayin mace mai kamar maza, mai yunkurin taimaka musu, agaza musu duk wani abu da kike da shi kina kokarin nuna musu idan aka yi kaza za a yi nasara ko rashin nasara.
Matan Arewa Ba Sa Yin Dogon Karatu
“Misali a nan Kano mun ga irin matan da ke fitowa takarar siyasa yawancinsu ba su yi dogon karatu ba, ba su yi dogon nazari ba kawai suna fitowa ne a matsayin sun fara yi kada-kadan ta takarar dan majalisa kuma tun can da ma ba za su iya ci ba kuma abin da ake jin shi ne ka fito da niyyar kai wa ga cimma gaci, ba kawai don ka fito don ka samu dan kwabbanka ka koma ba.
“Duk wanda yake irin wannan siyasar ba ya samun nasara saboda idan ka fito yau ka fito gobe za a ce wane bai ma san me yake ba.”
Ya Kamata Mutane Sun Sauya Tunaninsu A Kan Matan Da Ke Yin Siyasa
Hafsat, wadda an dama da ita a harkokin siyasa ta ce kallon da al’umma ke yi wa duk macen da ta shiga na taka muhimmiyar rawa wajen sanya mata damba tsakaninta da siyasar, ma’ana kallon mace a matsayin ‘yar iska ko wani abu na daban na sanyawa ta janye jiki da siyasar duk da irin tarin gudunmawar da take da ita.
“Duk macen da ta fito ta jajirce tana hulda irin wannan tun da an san siyasa abu ne na maza, to idan kika fito kina cikin maza za a ke miki kallo na daban.
“A matsayinmu na Hausawa sannan akwai al’ada da addini da suka bukaci mace ta zauna waje daya wanda hakan daidai ne amma zamani da ci gaba ya zo da abubuwa daban-daban.
“Ya kamata mutane su canja tunaninsu akan irin matan da suke yin siyasa, misali Allah ya jikan Maman Taraba ba irin maganar da ba a fada a kanta ba, wani ma zai kirkiri sharri da karya ya yi a kansu.
“Wannan kuwa ba abin da yake kawo mana sai ci baya, saboda idan ka ilimantar da mace gaba daya al’umma ka ilimantar.
“Dole ne a sauya irin tunanin da ake yi a kan matan da ke yin siyasa ‘yar iska ce.”
Mata Sun Fito Siyasa, Amma Ba Su San Mene ne Manufarta Ba. Shi kuwa Salman Yahuza sako ya turo, ya bayyana cewa “Da mata za su bada hadin kai da za a sauya kasar nan sai dai matan su kan fito siyasa amma ba su san mene ne manufarta ba domin ra’ayin mazajensu da ‘yan uwansu suke bi.
“Kamata ya yi a ce kowace mace ta fito da kuduri don ta yi amfani da shi sannan su sa hankali wurin zaben wanda wanda ya fi cancanta,” kamar yadda Salman ya aike da na shi sakon ke nan.
Mata Su Ne Makiyan Kansu
Wani mai suna Welfare cewa ya yi mata su ne makiyan kansu a kan harkar siyasa.
“Kowa da kuri’arsa ya dogara idan aka ce mata za su fito su zabi kansu ko mara wa wani ko wata baya ba inda ba za su je ba.
“Amma saboda kiyayya a tsakaninsu sai ka ji ana wance ce fa sai ka ga da kansu suna dakushe kansu da kansu. Dole ne su koma teburin sulhu, misali idan ka duba kaf Arewa mace daya ce Sanata, ita ce Sanata Aisha Binani wadda take neman takarar gwamna.
“Gaskiya kalubalen rawar mata a siyasa ya fi yawa a Arewa saboda ana ganin bai dace mace ta shiga a dama da ita ba, to yaya zamu fara ba su gudunmawa sannan ba za a zabi ki saboda ke mace bace, a’a sai kin zo da muradun da jama’a ke son cimma.
“Ma’ana zan yi kaza, zan yi kaza za a baki dama idan har kin zo da abin da ake so ko ya fi na abokin takararki, amma ki zo da cewar ke mace ce bana tunanin wannan zai yi aiki.
“Akwai bukatar a dinga bai wa matan shawarar su dinga zuwa da abu wanda ya dace. Don haka sai sun sake komawa tebur don sake fasalin siyasarsu.”
Mata Su Daina Buya A Bayan Maza, Su Fito A Dama Da Su
Nuru IB Shekh, ya ce mata suna yin siyasa amma ba sa fitowa su yi da kansu saboda rauni da suke da shi.
Har ila yau, ya ce akwai bukatar bai wa matan dama don a dama da su don mulki ba iya maza ne ya kamata suke yi ba.
“Shi alkairi yana zuwa ne ta bangaren mata da maza ne baki daya don haka dole ne su daina buya a bayan maza su fito su ma a dama da su.”
Mata Su Kasance Masu Ra’ayin Kansu
Shi kuwa Farouk Ilelah, ya ce abu daya ne ya kamaci mata da su yi, shi ne wayar da kansu abin da yake da akwai kan rawar da za su taka a siyasa a yanzu, saboda kusan kaso 60 na masu zabe mata ne.
“Ya kamata mace ta da zama mai ra’ayin kanta tun kafin ta je filin zabe, kuma kada ta bari a karkara akalarta don sayen kuri’arta don haka na iya jefa mu cikin wahala.
“A wasu lokuta matan ne ke bamu matsala a lokutan zabe saboda sna saurin sauya tunaninsu dole ne ko da an ba su wani abu amma su zabi wanda ya cancanta don su ma a dama da su s gaba.”
Wato ita siyasa duk wanda zai shige ta yana bukatar jajircewa walau mace ko namiji, don aba ce da ke tarin kalubale musamman idan aka yi duba da irin yadda ‘yan mazan jiya suka sha gwagwarmaya.