Kungiyar tuntuba ta Arewacin Nijeriya (ACF) ta yi Ikirarin cewa, ba za ta sake cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari uffan ba kan rashin tsaro.
Sakatare Janar na kungiyar, Murtala Aliyu ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar inda ya ce muna bukatar Buhari ya kara mayar da hankali wajen zuba kudi don magance kalubalen tsaron.
Aliyu ya yi nuni da cewa, a ‘yan watannin baya, kalubalen ya kara munana musamman ganin yadda ake kara samun gungun ‘yan Bindiga da masu rajin a raba Nijeriya.
Ya kara da cewa, ko da yake, ACF za ta iya saka kanta a cikin jerin magoya baya na masoya Gwamnatin Buhari kuma ako da yaushe, muna yiwa Gwamnatin fatan nasara amma a yanzu ba za mu iya ci gaba da cewa Buhari uffan ba kan abin da bai so a sanar da shi.
Aliyu ya ci gaba da cewa, fasa gidan gyara hali na Kuje na kwanan wanda yayi sanadiyyar arcewar wasu Fursunoni ciki harda ‘yan Boko Haram dake tsare a Gidan, ya jefa tsoro a zukatan ‘yan Nijeriya.
hakan nan kuma, ‘yan Bindiga sun kai wa ayarin motocin Buhari hari akan hanyar su ta zuwa garin Daura mahaifar Buhari don halartar shagulgulan bikin babbar Sallah ta bana.
A ranar 28 ga watan Maris, ‘yan bindigan sun farmaki jirgin kasan Abuja zuwa Kadun, inda hakan ya janyo aka sace fasinjoji da dama tare da hallaka wasu.
Irin wadannan hare-haren, ya tilastawa wa ‘yan Nijeriya shakku a zuciya inda suke ci gaba da tambaya shin yau she ne Gwamnatin za ta lalubo da mafita kan kalubalen?