• English
  • Business News
Tuesday, September 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamata Ya Yi NATO Ta Daina Hura Wutar Rikicin Rasha Da Ukraine

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Kamata Ya Yi NATO Ta Daina Hura Wutar Rikicin Rasha Da Ukraine
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, abin da ya kamata kungiyar NATO ta yi shi ne ta binciki kanta, maimakon shafawa kasar Sin bakin fenti kan rikicin Rasha da Ukraine.

Kakakin ya bayyana haka ne a yau Talata, a yayin taron manema labaru da aka saba yi kullum.

  • Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Ci Gaba Da Farfadowa Tare Da Nuna Kyakkyawar Yanayi A Watan Mayu
  • Sojoji Na Kan Bakarsu Na Tabbatar Da Tsaron Kasa – Shugaban Tsaro

An ba da rahoton cewa, sakatare janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya yi gargadi a jiya Litinin, inda ya ce idan kasar Sin ta ci gaba da ba wa kasar Rasha fasahar soja, da kuma taimakawa kasar a rikicin da take da Ukraine, kasashen NATO za su sa kasar Sin ta “dandana kudarta”.

Game da haka, Lin Jian ya kara da cewa, ba kasar Sin ce ta kirkira ko kuma ta shiga cikin rikicin na Ukraine ba, kuma a ko da yaushe tana himmantuwa wajen sa kaimi ga yin shawarwari cikin lumana, kana matsayin da kasar Sin ke dauka na adalci da gaskiya da muhimmiyar rawar da take takawa kan batun, na samun amincewa daga kasashen duniya.

Baya ga haka, dangane da ganawar da za a yi tsakanin ‘yan majalisar dokokin Amurka da Dalai Lama, da kuma yadda Amurka ta zartar da wani kudurin doka mai alaka da Xizang, kakakin ya bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka da ya mutunta kudurin da ya dauka na amincewa da Xizang a matsayin wani bangare na kasar Sin, kuma ba zai goyi bayan neman ‘yancin kan Xizang ba, haka kuma, kada ya rattaba hannu kan wancan kudurin doka. Ya ce kasar Sin za ta dauki kwararan matakai masu inganci don kare muradunta na mulkin kai, tsaro, da kuma ci gaba. (Bilkisu Xin)

Labarai Masu Nasaba

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkaJapanSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kasar Sin Ta Kaddamar Da Matakan Gaggawa Kan Ambaliyar Ruwa A Larduna 3 Da Mamakon Ruwan Sama Ya Afkawa

Next Post

Yawan Kudin Da Sin Ta Zuba Kan Manyan Ababen Zirga-Zirga a Ko Wace Rana Ya Kai Yuan Biliyan 10.7 a Shekarar 2023

Related

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

10 hours ago
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
Daga Birnin Sin

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

11 hours ago
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
Daga Birnin Sin

Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”

12 hours ago
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin

13 hours ago
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”
Daga Birnin Sin

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”

14 hours ago
Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet

16 hours ago
Next Post
Yawan Kudin Da Sin Ta Zuba Kan Manyan Ababen Zirga-Zirga a Ko Wace Rana Ya Kai Yuan Biliyan 10.7 a Shekarar 2023

Yawan Kudin Da Sin Ta Zuba Kan Manyan Ababen Zirga-Zirga a Ko Wace Rana Ya Kai Yuan Biliyan 10.7 a Shekarar 2023

LABARAI MASU NASABA

Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana

Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana

September 16, 2025
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa

September 16, 2025
Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne

September 15, 2025
Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 

Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 

September 15, 2025
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu

September 15, 2025
Tinubu

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata

September 15, 2025
Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”

Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”

September 15, 2025
Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa

Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa

September 15, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin

September 15, 2025
Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 

Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 

September 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.