Kamfanin kera jiragen sama na Turai wato Airbus, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya a ranar Alhamis, tare da abokan huldar sa na kasar Sin, a kokarin gina sashen hada jirage na biyu a wurin da yake aiki a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, wanda zai kara karfinsa na hada jirage samfurin A320.
Sabon wurin hada jiragen, zai taimakawa burin da Airbus ke da shi na kera jiragen sama samfurin A320 guda 75 a kowane wata nan da shekarar 2026.
Bayanai na cewa, yanzu haka akwai wuraren hada jiragen sama dangin A320 guda 4 ne a duk duniya, wato wadanda ke Toulouse a Faransa, da Hamburg a Jamus, da Mobile a Amurka, sai kuma wanda ke birnin Tianjin na kasar Sin.(Ibrahim)