Babban kamfanin fasahar nan na Amurka wato Apple, ya sanar da shirinsa na zuba jarin da ya kai kudin Sin yuan miliyan 720, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 100.31, a fannin samar da makamashi mai tsafta da ake iya sabunta amfani da shi a kasar Sin.
Wata sanarwa da kamfanin ya fitar a Litinin din nan, ta ce kudaden jarin za su samar da damar kara yawan megawatt duk sa’a kusan 550,000 na lantarkin da ake samarwa ta iska, da hasken rana duk shekara, cikin jimillar lantarkin kasar Sin, adadin da kuma ake fatan karuwarsa yayin da masu zuba jari suka karu.
Kazalika, sanarwar ta hakaito babban jami’in gudanarwa na kamfanin Jeff Williams, na cewa yanzu haka masu samarwa kamfanin Apple kayayyakin harhada hajojinsa a kasar Sin na kan gaba wajen samar da ci gaban fasahohi masu nasaba da na’urori masu kwakwalwa, da fannin makamashi mai tsafta.
Williams ya kara da cewa, sakamakon kaddamar da kudaden jarin na wannan karo, kamfanin Apple na fatan kara zurfafa hadin gwiwarsa da sassan masu samar masa da kayayyaki na Sin, ta yadda za a kai ga ingiza kirkire-kirkire domin cin gajiyar dukkanin duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp