Kamfanin jiragen sama mai zaman kansa na Air Peace a Nijeriya ya bayyana aniyarsa na kwashe ‘yan Nijeriya da rikicin kasar Sudan ya rutsa da su kyauta idan har gwamnatin tarayya za ta iya kai su filin jirgin sama mai aminci da tsaro a kowacce kasa da ke makwabtaka da Sudan.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Litinin da ta fito daga shugaban kamfanin kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin, Allen Onyema.
Ya bayyana cewa daliban da sauran ‘yan Nijeriya wadanda suka makale a cikin kasar da ke fama da yakin suna bukatar taimakon kamfanin cikin gaggawa.
“Air Peace a shirye yake ya kwashe ‘yan Nijeriya da suka makale a Sudan kyauta idan gwamnati za ta iya kai su filin jirgin sama mai aminci da tsaro a kowacce kasa da ke makwabtaka da Sudan. Bai kamata ace komai gwamnati ce kadai zata yi ba.
“A shirye muke mu yi gaggawa kuma babu bata wani lokaci. Duk wani aiki da zai daga martabar kasa, hadin kan kasa, zaman lafiya da hadin kai, to bamu shakkar aikata wa, aikin ne gabanmu.
“Har ila yau, ba mu yin da nasanin zama ‘yan Nijeriya duk da fuskantar wasu kalubale a kasar. Idan aka kai daliban wata kasa, kamar Kenya ko Uganda, za mu shiga kasar don kwashe mutanenmu. Wasu iyaye sun fara kira gare mu da mu taimaka. A shirye muke mu sake yin taimakon da muka saba yi,” inji shi.