A yau ne, aka mikawa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na China Eastern da ke birnin Shanghai, jirgin sama na C919 na biyu da kasar Sin ta kera.
Wannan shi ne jirgi na biyu cikin jiragen saman na C919 guda biyar da kamfanin zirga-zirgar jiragen saman China Eastern ya saya daga kamfanin da ya kera shi, wato (COMAC) tsari iri daya da na farko
Ya zuwa ranar 12 ga watan Yuli, jirgin farko na C919 ya gudanar da zirga-zirgar kasuwanci 87 na kimanin sa’o’i 250, ya kuma samarwa fasinjoji 11,095 hidima. (Mai fassara: Ibrahim)