shugaban zartarwa na kamfanin wutar lantarki na ‘Kaduna Electric’, Engr. Yusuf Usman Yahaya, ya yi gargadi da kakkausar murya ga jama’a cewa kamfanin ba zai sake lamuntar hare-haren da ake kaiwa ma’aikatansa ba.
Ya ce daga yanzu duk al’ummar da ta ci zarafin ma’aikatan wutar lantarki na Kaduna Electric a yayin da suke gudanar da ayyukansu na halal, to za su fuskanci fushin kamfanin ta hanyar dakile musu wutar lantarki sabida rashin aminci ga ma’aikatansu a wurin al’ummar wannan yankin.
Shugaban ya bayyana hakan ne ayau a wani taron tattaunawa da wakilan abokan cinikin kamfanin daban-daban a Rigasa, Kaduna, wadanda suka ziyarci hedikwatar Kaduna Electric.
Engr. Yusuf ya koka kan lamarin da ya faru a garin Kabala inda aka ci zarafin wasu ma’aikata inda ya ce kamfanin ya rubutawa shugabannin hukumomin tsaro da hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya bayanin dalilin da ya sa ya janye ayyukansa daga cikin al’ummar yankin. Ya ce kamfanin ba zai huta ba har sai an gurfanar da masu laifin a gaban doka.