A kokarin karya mamayar da kamfanin talabijin na kudi Multichoice ya yi a Nijeriya, an samu wani kamfani mai suna Metrodigital Limited, wanda kamfani ne da ke da alaka da kamfanin Silber Lake Telebision (SLTB), ya fito da sabbin tsare-tsare da zai kai ga karya yadda kamfanin Multichoice ya zama wa masu hulda da shi karfen kafa.
A yayin kaddamar da fara aikin watsa labarai na kamfanin da aka yi a Abuja a karshen mako, Shugaban kamfanin, Ifeanyi Nwafor ya karfafa bukatar ganin an karyar yadda Multichoice ya mamaye fagen harkar talabijin na kudi a Nijeriya ta hanyar karya kudin da suke karba a hannun masu hulda da su tare da kuma samar da ingataccen aiki da al’umma za su amfana.
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Zanta Da Takwaransa Na Tanzania
- Wike Ya Ba Shugaban Ƙasar Sanigal Bassirou Faye Shaidar Zama Ɗan Ƙasa A Abuja
Ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya sun yi maraba da zuwan su, musamman ganin za su samu sauki da kuma karin kafafen kallo fiye da abin da suke samu a hannun Multichoice duk da dimbin kudaden da suke karba.
“Ina fatan wasu kamfanoni za su shigo domin bayar da nasu gudummawar, ‘yan Nijeriya sun yi murnar karya mamayar da Multichoice ya yi, zaka iya komawa wani kamfani kuma ka samu abin da kake bukata ba tare da ka biya kudade masu yawa ba.,” in ji shi
Mista Nwaforya kuma kara da cewa, kamfanin SLTB a shirye yake na ba masu hulda da shi dukkan abin da zai sa su ci gaba da kasancewa da su, ya kuma yi kira ga wasu kamfanonin yada labarai da su shigo don a dama da su a Nijeriya.