Kamfanin mai na Nijeriya (NNPCL), ya yaba da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na cire tallafin man fetur.
A cikin umarnin farko na manufofin gwamnatinsa, Shugaba Bola Tinubu, a ranar Litinin, ya bayyana sanarwar cire tallafin man fetur nan take.
Ya bayyana hakan ne a jawabinsa na farko a matsayin sabon shugaban Nijeriya na 16.
Bayan wani taron gaggawa da aka yi a Abuja, Babban Daraktan Rukunin (GCEO) Kamfanin man fetur na kasa, NNPC Limited, Mallam Mele Kyari, ya bayyana cewa, tallafin man fetur shi ke kwashe wa kamfanin kudadensa amma cire tallafin yanzun, zai samar wa kamfanin da kudade da zai gudanar da ingatattun ayyuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp