Kamfanin kera manyan motocin dakon kaya na kasar Sin Sinotruk ya kaddamar da motocinsa kirar H2 mai dakon kaya marasa nauyi da ta H3 ta dakon kaya masu matsakaicin nauyi a kasar Kenya, tare da kamfanin CFAO Mobility a matsayin mai rarraba motocin a cikin gida.
Babban manajan kamfanin CFAO Mobility na Sinotruk Sarfraz Premji, ya shaida wa manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, an kera samfuran motocin ne ne don kawo sauyi ga masana’antar sufuri saboda suna iya daukar kaya masu nauyi, sannan an sa musu manyan tankunan mai, inda hakan zai rage bukatar yawan zuwa shan mai da kuma ba da damar daukar dogon lokaci ana tafiya, kana wannan zai rage yawan kudin da ake kashewa wajen shan mai.
Premji ya ce “bisa tabbatar da ingancin dogaro da su da kuma karkonsu na dogon lokaci, wadannan manyan motocin sun zamo na daban da babu irinsu kuma ababen zabi a cikin nau’o’in manyan motoci masu dakon kaya masu karami da matsakaicin nauyi.”
Ya kuma yi nuni da cewa, ana samun karuwar rungumar manyan motocin kasar Sin a kasuwannin kasar Kenya ne, saboda suna dacewa da titunan mota na Afirka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp