Ma’aikatar kwadago ta kasar Amurka (DOL) ta bayyana cewa, daya daga cikin manyan kamfanonin kula da tsaftar abinci na kasar, ya dauki yara sama da 100 aiki masu hadarin gaske.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar jiya Jumma’a na nuna cewa, kamfanin Packers Sanitation Services Inc. (PSSI), mai hedkwata a birnin Kieler na jihar Wisconsin, ya nuna cewa, kamfanin ya biya dalar Amurka miliyan 1.5 a matsayin diyya, bayan da wani bincike na ma’aikatar DOL ya gano cewa, kamfanin ya dauki a kalla yara 102 aiki, masu shekaru 13 zuwa 17 da haihuwa ayyuka masu hadari kuma ya sa su yi aikin dare a wuraren sarrafa nama 13 a cikin jihohi 8 na kasar.
Yaran dai na suna aiki da sinadarai masu hadari da kuma na’urorin tsaftace nama da suka hada da zarto, da doguwar wuka, da wuka mai baki biyu, kamar yadda binciken da aka fara a watan Agustan shekarar 2022 ya nuna.
Amurka ita ce kasa daya tilo a duk duniya da ba ta amince da yarjejeniyar kare hakkin kananan yara ta MDD ba, yarjejeniyar da aka fi amincewa da ita tun bayan kaddamar da ita a shekarar 1989.(Ibrahim)