Kamfanin XD na kasar Sin, ya sanya hannu tare da gwamnatin kasar Sudan, kan kwangilar gina tashar samar da lantarki a birnin Al-Fula, fadar mulkin jihar Kordofan ta yamma, a wani mataki na hade biranen jihar da manyan turakun lantarki na kasar.
Da yake tsokaci yayin bikin sanya hannu kan kwangilar, ministan kudin Sudan Jibril Ibrahim, ya ce yayin taron baya bayan nan na Sin da kasashen Larabawa da ya gudana a birnin Riyadh na Sudiyya, Sin ta alkawarta fadada kawance da Sudan. Don haka fatansa shi ne ganin alakar sassan biyu ta taimakawa Sudan wajen bunkasa samar da ababen more rayuwa, da samun bunkasuwa a dukkanin fannoni. Ya ce ana sa ran kammalar wannan muhimmin aiki, wanda zai lashe dalar Amurka miliyan 9.4 cikin watanni 6.
Ana kallon wannan aiki a matsayin da ya daga mafiya muhimmanci a fannin fadada samar da lantarki a Sudan, ana kuma fatan tashar lantarkin ta Al-Fula, za ta samar da lantarki da zai kai karfin megawat 450, kana za ta ba da lantarki ga mafi yawan sassan jihar Kordofan ta yamma dake kudu maso yammacin kasar ta Sudan. (Saminu Alhassan)