Da alama kamfanin kayan shafe-shafe na kasar Singapore mai suna Fonty, ya samu riba mai tarin yawa daga halartar bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin tsawon shekaru 6 a jere, a shekarar farko na bikin, kamfanin ya sayar da kwalaye kasa da 200, amma yanzu ya sayar da kusan dubu 200 a shekara.
A yau ne aka kammala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) karo na 6, inda aka yi kiyasin samun kudin shiga da ya kai dalar Amurka biliyan 78.41 a duk shekara, adadin da ya karu da kashi 6.7 bisa 100 idan aka kwatanta da bikin na baya, wanda kuma ya zama sabon matsayi. A yayin baje kolin, kamfanoni 3486 daga kasashe da yankuna 128 ne suka halarci bikin baje kolin kasuwanci, adadi mafi girma da aka taba samu.
Baje kolin na kasa ya samar da wani muhimmin dandali ga kasashen da ke da matakai daban-daban don inganta mu’amula da inganta hadin gwiwa, da cimma moriyar juna da nasara tare, kuma kasashen da suka halartar baje kolin sun yaba matuka. Shekara bayan shekara, bikin na CIIE yana haifar da sabon ci gaba ga bude kofar raya tattalin arzikin duniya da hadin gwiwa tare da samar da sabbin nasarori. (Mai fassara: Ibrahim)