Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa(CIIE) karo na 8 da ke gudana yanzu haka a birnin Shanghai na kasar Sin, ya baje kolin sabbin kayayyaki da fasahohi da ma hidimomi har 461, wasu daga cikinsu kuma sun kasance karon farko ke nan da ake nuna su a duniya ko a nahiyar Asiya, ko kuma a kasar Sin. Cikakken zama na hudu na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 da aka gudanar ba da jimawa ba a birnin Beijing, ya nuna alkiblar raya tattalin arziki da zaman al’umma a kasar cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma kamfanonin kasa da kasa sun gano karin damammaki daga cikin matakan da za a dauka, musamman ma “gaggauta dogaro da kai wajen bunkasa kimiyya da fasaha da raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko”, da “inganta tushen bunkasa tattalin arziki da ke shafar hajoji na zahiri”. Kuma sabbin kayayyaki da fasahohin da ake baje kolinsu a bikin CIIE na wannan karo, ya ba wa kamfanoni masu jarin waje matukar kwarin gwiwa.
“Kasuwar kasar Sin ta zamanto muhimmiyar kasuwa a gare mu. Mun yi hasashen a cikin ’yan shekaru masu zuwa, kamfaninmu zai rubanya harkokinsa a kasar Sin, har ma za mu yayata fasahohin da muke samu daga kasar Sin zuwa fadin duniya”, in ji Sandeep Seth, babban jami’in kamfanin Tapestry na kasar Amurka.
Sabbin fasahohin da ake baje kolinsu a bikin CIIE, dauke suke da burin da ake da shi ga samar da rayuwa mai dadi, wadanda kuma suka shaida yadda kamfanoni masu jarin waje da kasar Sin ke rungumar juna. Kamar dai yadda manyan jami’an kamfanoni masu jarin waje da dama suka bayyana fatansu na ci gaba da dukufa a kan bunkasa ayyukansu a kasar Sin, hakan na nuna kakkarfan kudurinsu na tsayawa a nan kasar.














