• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanonin EV Na Kasar Sin Ba Sa Dogaro Da Tallafi

by CGTN Hausa
2 years ago
Ev

Wang Wentao, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana a jiya Lahadi cewa, saurin bunkasuwar kamfanonin kera motocin lantarki (EV) na kasar Sin, sakamakon kirkire-kirkiren fasahohin zamani ne, da kyakkyawan tsarin samar da kayayyaki, da ingantacciyar takara a kasuwa, ba tallafi ba. Zargin da Amurka da Turai ke yi na samar da motocin fiye da kima ba shi da tushe, a cewarsa.

Zargin da Washington da Turai suka yi na barazanar “girman karfin masana’antun” na kasar Sin wajen samar da hajoji fiye da kima da kuma zargin rashin adalcin cinikayya da kamfanonin Amurka da Turai, ya samo asali ne daga maganganunsu masu tayar da hankali da kuma zurfin rashin fahimta game da kasuwar kasar Sin. Amurka na ganin cewa sassan tattalin arzikin kasar Sin na samun goyan baya da tallafi na wucin gadi, kuma yana rage damammakin ga bunkasuwar kasuwannin Amurka har ma da kawar da ayyukan yi. Yayin da a hakikanin gaskiya, kasar Sin ba ta taba tsunduma cikin harkokin cinikayyar da ba ta dace ba ko nuna son kai ga kamfanoni ba. Kasar Sin ita ce jagora a fannin samar da motocin lantarki wato EV, na’urorin hasken rana, batura, saboda kwarewarta da dorewar sabbin kirkire-kirkirenta, da karuwar bukatun hajojinta daga ko’ina cikin duniya. Hajojin kasar Sin masu inganci suna da fifiko sosai a kasuwannin duniya kuma suna biyan bukatun abokan cinikayya a ketare.

  • Gwamnan Bauchi Ya Bai Wa Ma’aikatan Jihar Goron Sallah Na N10,000 Ga Kowanne
  • Roxy Danckwerts: Ina Matukar Son Rungumar Pandar Kasar Sin

Duk wanda ya lura da karfin tattalin arzikin kasar Sin, ko shakka babu zai fahimci cewa, kasar na bin tsarin ‘yancin cinikayya, da ka’idojin WTO, da tsarin cinikayya na duniya. Kasar Sin ba za ta taba yin amfani da dabarun kasuwancin da ba su dace a kan kamfanonin ketare ko kuma ta yi babakere ba.

Ban da haka, bunkasuwar masana’antun EV na kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen tinkarar sauyin yanayi a duniya, da samar da sauye-sauye don kiyaye muhalli da rage hayakin Carbon mai dumama yanayi. (Yahaya)

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
An Amsa Tambayoyi Game Da Ziyarar Da Sakatariyar Baitil-malin Amurka Ta Gudanar A Sin

An Amsa Tambayoyi Game Da Ziyarar Da Sakatariyar Baitil-malin Amurka Ta Gudanar A Sin

LABARAI MASU NASABA

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.