“Kasar Sin tana cikin fiye da kashi 90% na ayyukan bincike da samarwa na duniya.” Kuma “Tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin ya zama ginshikin daidaita samar da kayan aikin likitanci a duniya…” A bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa na kasar Sin karo na uku, shugabannin kamfanonin harhada magunguna da dama na kasa da kasa kamar su Medtronic, da Sanofi, da GE Healthcare, sun bayyana cewa, za su kara habaka tsarinsu a fannin kirkire-kirkire a kasar Sin, da kuma cin gajiyar kasuwar kasar Sin yadda ya kamata.
An rufe bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya wato CISCE karo na uku na tsawon kwanaki 5 a yau. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp