Shugaban Kenya William Ruto, ya kaddamar da wani kamfanin da zai rika samar da wayoyin salula na zamani, wanda hadin gwiwa ne tsakanin kamfanonin sadarwa na kasar Kenya, wato Safaricom da Jamii Telecom, da kuma kamfanin Shenzhen TeleOne Technology na kasar Sin jiya Litinin.
Shugaba Ruto ya ce, kamfanin harhada naurori na gabashin Afirka dake Kenya (EADAK) wanda ke garin Athi River, kimanin nisan kilomita 28 kudu maso gabashin Nairobi, babban birnin kasar Kenya, zai rika kera wayoyin hannu miliyan uku a duk shekara. Yana mai cewa, Kenya za ta ci gajiyar samar da ayyukan yi ga jama’arta, baya ga wayoyin salula na zamani masu araha.
Don haka, ya yaba da hadin gwiwar dake tsakanin masu zuba jari na kasashen Kenya da Sin, ganin yadda kamfanin da ake fatan kafawa, zai karfafa matsayin kasar Kenya a matsayin babbar cibiyar tattalin arziki na zamani da kuma jagora a fannin fasaha da kirkire-kirkire. (Mai fassara: Ibrahim)