Hukumar kula da shaidar ‘yan kasa (NIMC) ta tabbatar da cewa, a yanzu Kamfanonin sadarwa na iya tantance lambar shaida ta dan kasa (NIN) domin yin sabuwar rajistar SIM, dawo da tsohon SIM, da dai sauransu.
Hakan, ya biyo bayan nasarar kaura da NIMC ta yi ta zuwa NINAuth, sabon dandalin tantancewar NIN.
Wannan ya nuna wata babbar nasara wajen haɓaka tsaro, inganci, da kuma saukaka amfani da manhajar don tabbatarwa da tantance NIN.
Dandali na NINAuth, wanda NIMC ya tsara kuma ya aiwatar, yana bayar da damar tantance bayanan ‘yan kasa ta hanya mafi dacewa da aminci don tabbatar da asalinsu.