Kanada ita ce babbar makwabciyar Amurka kuma abokiyar kawancenta. Amma idan ana maganar moriya, Amurka ba ta da tausayi wajen cin zarafi, tilastawa da kuma wulakanta Kanada.
Kanada na daya daga cikin kasashen farko da aka yi wa barazanar karin haraji a lokacin wa’adin farko na shugaban Amurka Donald Trump. Bayan sake zabensa, Trump ya sha yin barazanar “mallakar” Kanada tare da mayar da ita zuwa jiha ta 51 ta Amurka.
- Gwamnatin Tarayya Ta ƙaryata Zargin Tigran Gambaryan Kan Jami’an Gwamnatin Nijeriya
- “Ne Zha 2” Ya Zama Fim Din Kasar Sin Na Farko Da ya Samu Zunzurutun Kudi Yuan Biliyan 10
A farkon watan nan, Amurka ta yi barazanar sanya karin harajin kashi 25 cikin dari kan kayayyakin da ake shigar da su Amurka daga Kanada bisa dalilan Fentanyl da bakin haure. Kwanan nan, Amurka ta sanar da kara harajin kashi 25 cikin dari kan karafa da gorar ruwa da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, inda Kanada ta kasance ta farko da abin ya shafa.
A bangare guda, ‘yan siyasar Kanada suna fama da walakanci daga Amurka, amma kuma sun damu da lalacewar muradunsu, a dayan bangare kuma, ba su da karfin “yaki” da Amurka, don haka sun fito da wata dabara, wato nuna adawa da Sin da kuma yi mata batanci, ta yadda suke fatan Amurka za ta saukaka matsin da take yi wa kasarsu. Kwanan nan, gwamnonin dukkan larduna da yankuna 13 na Kanada sun je Amurka a cikin wata tawaga, suna kokarin rokon bangaren Amurka da su “yi sassauci”. Wani abin mai ban dariya shi ne, wadannan ‘yan siyasar Kanada sun yi amfani da “Batun kasar Sin” don shawo kan Amurka, inda suka bayyana Sin a matsayin “makiyayyar tattalin arziki ta gama gari”.
“Batun Sin” ba zai iya zama “garkuwa” ga Kanada ba. “Zama makiyin Amurka na da hatsari, amma zama abokin kawancen Amurka abu ne mafi mummuna”, in ji Henry Alfred Kissinger. A yanzu, ya kamata ‘yan siyasar Kanada su kara fahimtar wannan furucin da Kissinger ya yi. (Safiyah Ma)