• English
  • Business News
Thursday, May 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kananan Sana’oi Da Ci Gaban Kasa (4)

by Hussaini Najidda Umar
3 years ago
in Sana'a Sa'a
0
sana'a
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ci gaba daga makon da ya gabata

Kafin na ci gaba da tattauna abin da na fara a makon da ya gabata, Mallam Rabi’u Indabawa na jaridar LEADERSHIP HAUSA, ya nemi na yi wa masu karatu bayani kan banbance tsakanin ‘Ciniki da Kasuwanci’ to, abin da ake nufi da Ciniki shi ne tattaunawar da ake yi da mai saye da sayarwa a wajen kasuwanci.

Misali ka zo kasuwa ka ga kayayyaki iri-iri sai ka tambayi mai kayan nawa yake sayarwa, to wannan tattaunawar da za ku yi har a sami matsaya ka sa ya ka tafi shi ne ciniki.

  • Sashin Blue Line Na Layin Dogo A Legas Ya Zama Wani Muhimmin Aikin Dake Shaida Hadin-Gwiwar Sin Da Najeriya

Wato a taKaice tattaunawa da ake yi da mai kaya da mai saye shi ne ciniki. Sannan kasuwanci kuma a nan nufin buKata, misali a hadu a wani guri da aka ware don saye da sayarwa ko kuma a cikin gida tun da ita kasuwa ba dole sai fili ko wani guri ba, a’a ita kasuwa tana nufin buKata, shi kuma wanda yake neman wannan abin da kai kake da shi sai ka zo ku yi yarjejeniya ka saya a wajensa ya sayar maka.

Wannan shi ne dan Karin bayani da zan yi game da tambayar da Mallam Rabiu Indabawa ya yi, amma Allah ne masani. Kaima mai karatu idan kana da abin da zaka Kara na bayani game da wadannan kalmomi muna maraba da gudumawarku.

Labarai Masu Nasaba

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi

A makon da ya gabata na yi tsokaci a kan menene Kananan sana’oi da yadda rabe rabensu yake. Da fatan mai karatu ya fahimta an san inda wannan darasi namu ya sa gaba. Abin da nake so a kuma fahimta kuma shi ne na dauki wannan batu ne na Kananan sana’oi domin mutane su fahimta cewa su irin wadannan Kananan sana’oi su ne Kashin bayan ci gaban duk wata Kasa a duniya.

Saboda kamar yadda na fada a makon da ya gabata irin wadannan sana’oi ko kamfanoni su ne suke ba wa ‘yan Kasa bila adadin aikin yi domin gwamnatocinmu ba za su iya ba wa kowa aiki ba. Shi ne ya sa Kasahen duniya a kullum suke kuma bijiro da abubuwa na jin dadi don tallafa wa irin wadannan sana’o’i ko masu sana’oi.

Miliyoyin kudade ko na ce biliyoyin kudade suna juyawa kullum a cikin irin wadannan sana’o’i, saboda haka ya wajaba a garemu da mu fadakar da jama’a yadda ya kamata su kuma riKe sana’o’insu da mahimmacin gaske saboda su ne suke ba su abin da rayuwarsu take amfani da shi.

Idan za’a iya tunawa a shekarar 2020 annobar Korona ta yi wa duniya gaba daya wani mummunan kamu da kowa da kowa ya ji a jikinsa ciki kuwa har da masu Kananan sana’o’i. A Kasashen duniya daban-daban sun bijiro da shirye shirye don tallafa wa irin wadannan sana’oi ta yadda suka riKa fitar da kudade don biyan ma’aikatan irin wadannan sana’oi ko kamfanoni albashi.

Misali a Kasar Amurka, sai da aka shafe wata shida gwamnatin Amurka tana biyan Kananan kamfanoni ko sana’o’i kudade saboda kada su daina samun kudin kashewa. Kuma sun yi hakan ne don kada wadannan sana’oi su tsaya su daina aiki, saboda idan sun tsaya mutane da yawa za su ji jiki.

Haka kuma dokar kulle da aka saka lokacin Korona ta taba sana’o’i da yawa a duniya ciki har da Nijeriya. Shi ne dalilin da ya sa Kasashen duniyar suka KirKiri biyan kudaden albashi na musamman saboda kawai sun san cewa wadannan sana’oi ko Kananan kamfanoni su ne suke tafiyar da tattalin arziki ko wace Kasa a duniya.

Muma a Nijeriya gwamnati ta yi wannan KoKarin na KirKiro da shirin ‘surbibal fund’ wato biyan kudi ga Kananan ma’aikta da suke aiki a kmafanoni masu zaman kansu don rage radadin da hana fita da cutar Korona ta jawo wa al’ummar Kasa.

Mutane da yawa a Nijeriya sun samu kyautar Naira 30,000 na kimanin wata uku wato Naira 90,000 a jumlace. Wannan kuma haKiKa ta sa mutane da yawa ‘yan Nijeriya sun sami sauKi ta samun wannan kudaden.

Abu na gaba da zan kuma tattaunawa a nan shi ne shin ko wadannan Kananan sana’oin da ‘yan Nijeriya suke yi suna biya musu buKatunsu? A nan zan ce eh, suna biya musu sai dai kawai ba kamar yadda ake so ba. Musamman yanzu da abubuwa suka yi tsada saboda matasalar tashin kayyakin yau da kullum. Wannan kuwa dalilai ne masu yawan gaske da suka jawo wannan tsadar tun da ba wai kawai Nijeriya ba ce take fama da wannan matasalar har da sauran Kasashen duniya.

Wane abu ne mai Karamar sana’a ya dace ya yi a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa da tsadar kaya? Abin da ya kamata mai Karamar sana’a ya yi a wannan lokaci shi ne: Na daya, ya san me yake samu. Ina nufin shin kasuwancin nasa ya na bashi riba ko a’a, a nan ina so na fada wa mai karatu cewa akwai mutane da suke sana’a kullum amma ba su san me suke samu ba.

Saboda ba sa yin lissafin riba da faduwa. Shi ne ya sa sai ka ga dan kasuwa lokaci guda ya karye ya rasa menene dalili, dalilin kuwa shi ne, shi da kansa ne ya cinye duk ribar da yake samu a kasuwancinsa. Saboda haka ya zama dole mai sana’a ya riKa rubuta abin da yake samu a kullum.

Sannan kuma ya riKa sanin kullum idan ya tashi daga kasuwa me ya samu riba ko akasin haka. Duk dan kasuwa ba sai a fada masa yadda ya kamata ya yi lissafin ba domin ya sani. Saboda haka abu ne mai kyau mai Karamar sana’a ya san me yake samu kullum ta hake ne yake da ma’auni a hannunsa yadda kullum zai riKa auna kasuwancinsa.

Sannan abu na biyu shi ne dan kasuwa ya san inda kasuwacinsa yake so ya kai shi. A nan ina nufin duk wani mai yin sana’a ya rubuta a takarda manufofinsa da abin da yake so ya cimma a Karshe.
Misali, mutum zai shiga kasuwanci ya ce yana so ya tara miliyan goma a shekara biyu ko uku. A nan dan kasuwa shi ne zai zayyana hanyoyin da zai bi ya tara kudin. Sannan kuma ya rinKa bin duk wannan Ka’idojin da manufofin da ya rubuta. Ana so duk dan kasuwa komai kankantar jarinsa ya kasance ya na da manufa da burin inda yake so kasuwancinsa ya kai shi.

Akwai kamfanoni da yawa a Kasashen duniya da suka fara da kadan-kadan amma saboda sun yi tsari mai kyau da zayyana inda kasuwancinsu suke so ya je a shekarun da mutum ya tsara za’a ga wannan kamfanin ya kai.
Har ila yau, duk dan kasuwa ya sani cewa makomar kasuwancinsa tana hannunsa, a nan shi ne mai ruwa da tsaki ko mai wuKa da nama ta komai na kasuwancinsa.

Shi ne ya sa dole dan kasuwa ya yarda da kasuwancin da yake. Saboda yawancin ‘yan kasuwa suna yin kasuwanci amma ba sa son kasuwacin a ransu, shi ne dalilin da ya sa sai mutum ya ga kasuwancin nasa bai kai shi ko ina ba.
Dole ne mutum ya yarda da abin da yake kada a tambaye ka ka ce ‘to gamu nan dai wannan kasuwancin dai muna yinsa ne kawai’. Kada dan kasuwa ya rinKa fadar haka saboda yana nuna bai yarda da kasuwancin ba, shima kuwa kasuwancin ba zai yarda da shi ba.

Abu na ga ba shi ne, duk mai Karamar sana’a ya saka a ransa cewa wannan sana’ar ita ce rayuwarsa. A nan ina nufin sana’arka ta zamanto maka ita ce abokiyar rayuwa, yadda idan wani abu ya same ta ya sami rayuwarka.
Ta ya ya za’a mayar da kasuwanci ya koma abokin rayuwa?, hanya daya ce tak. Ka yarda a ranKa cewa idan babu ita babu kai. In dai ka yi haka to haKiKa kasuwancinka zai kai ka inda kake so musamman idan ka tsara manufofin masu inganci da kuma yiwuwa.

Kada ka KirKiri abin da ba zai yiwu ba. Kada ka zauna ka rubuta ka ce kana a kwana dari sana’arka ta tara maka Naira miliyan Dubu, idan ka yi haka to ka fara tambayar kanka nawa ne jarin da ka zuba da zai kawo maka Naira Biliyan dubu?
Wannan shi ne burin da ake cewa ba zai yiwu ba. A koda yaushe ka gina kasuwancinka a kan gaskiya da amana, saboda wadannan abunbuwan guda biyu su ne tushen ci gaban duk wani kasuwanci da mutum ya sa a ransa zai fara.

Sannan abu na Karshe mai son yayi kasuwanci, kada ka ko ki taba shiga kasuwancin da ba ka ko ki da ilimi a kai. Wannan shi ne babban kuskuren da mutane suke yi a yanzu na shiga kasuwancin da ba su da ilimi a kansa. Allah Ya kiyaye.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Dakarun Sojoji Sun Dakile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Mutane 3 A Kaduna 

Next Post

Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motocin Uwargidan Gwamnan Osun Hari

Related

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera
Sana'a Sa'a

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

3 months ago
Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi
Labarai

Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi

6 months ago
Akwai Dimbin Alhairi A Harkar Kasuwanci Na Kirifto – Khadija Ahmad
Labarai

Akwai Dimbin Alhairi A Harkar Kasuwanci Na Kirifto – Khadija Ahmad

9 months ago
Dangote Ya Soki Sabon Tsarin Gwamnatin Tinubu
Manyan Labarai

Dangote Ya Soki Sabon Tsarin Gwamnatin Tinubu

11 months ago
Shara
Sana'a Sa'a

Sarrafa Daskararriyar Shara

2 years ago
Halin Da Masu Kananan Sana’o’i Ke Ciki (3)
Sana'a Sa'a

Halin Da Masu Kananan Sana’o’i Ke Ciki (3)

2 years ago
Next Post
Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motocin Uwargidan Gwamnan Osun Hari

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motocin Uwargidan Gwamnan Osun Hari

LABARAI MASU NASABA

Lassa Da Shawara Sun Kashe Mutum 183 A Jihohi 36 Da Abuja

Lassa: Mutane 138 Sun Rasu, 717 Sun Kamu A Jihohi 18 – NCDC

May 15, 2025
Wa Suka Fi Cancanta A Nada Ministocin Tinubu?

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Dakarun Da Za Suke Tsaron Daji Don Yaƙar ‘Yan Ta’adda

May 15, 2025
ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed 

May 15, 2025
‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

‘Yansanda Sun Musanta Zargin Kai Wa ‘Yan Bindiga Abinci Ta Jirgin Sama A Kogi

May 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya

May 15, 2025
An Yi Wa ‘Yar Shekara 18 Fyade Har Lahira A Taraba

’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa

May 15, 2025
UTME

ASUU Ta Yi Barazanar Maka JAMB A Kotu Biyo Bayan Samun Mummunan Sakamako A UTME

May 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile

May 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa  Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista

May 14, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

Yadda Kasar Sin Ke Kokarin Gina Tashar Bincike A Sama Da Tubalin Kasar Duniyar Wata

May 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.