Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, a ranar Talata, ya bai wa wani rukunin mata 5,200 tallafin Naira miliyan 260 a karkashin shirin tallafawa na gwamnatin jihar.
An zaɓo wadanda suka amfana da shirin ne daga kananan hukumomi 44 na jihar.
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta gabatar da wasu matakai don tabbatar da cewa kudin ya isa ga wadanda aka shirya tallafin don su.
“Bayan gano alamun karkatar da kudaden tallafin a matakin farko, mun gabatar da matakai don tabbatar da cewa kudin ya isa ga wadanda aka yi niyya,” in ji shi.
Wasu daga cikin matakan da aka dauka sun hada da kafa kwamitin mambobi 20 a kowace karamar hukuma, wanda ya kunshi sarakunan gargajiya, shugaban karamar hukuma, shugaban jam’iyya, da sauran mambobi.
Ya yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kudaden ta hanyar kafa kananan kasuwancin kashin kansu domin inganta yanayin samun kudinsu da zamantakewarsu domin habaka tattalin arzikinsu da kuma na iyalansu.













